2027: Ana Rade Radin za a Sauya Shi, Matasa Sun Tara wa Ndume Kudin Fam
- Matasan Kudancin Borno sun fara tara miliyoyin Naira domin goyon bayan takarar Sanata Muhammadu Ali Ndume a 2027
- Sama da mutane 2,000 daga kananan hukumomi tara sun halarci taron tara kudin duk da raɗe-raɗin za a iya sauya Ndume
- Matasan sun jaddada aniyar tsaya wa kai da fata don sake mara wa Sanata Ali Ndume baya ya ci gaba da wakiltarsu a majalisa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jihar Borno – A wani gagarumin yunkuri na nuna goyon baya, dubunnan matasa daga mazabar Kudancin Borno sun hada Naira miliyan 38.5 domin tallafa wa kudirin wa’adi na biyar na Sanata Ali Ndume gabanin zaben 2027.
An gudanar da taron tara kudin ne a dakin taro na Forshams Hall da ke Maiduguri, inda sama da mahalarta 2,000 daga dukkannin kananan hukumomi tara na yankin suka halarta.

Source: Facebook
Arise News ta wallafa cewa mafi yawan wadanda suka bayar da gudunmawar sun hada da kungiyoyin matasa da kungiyoyin al’umma da ke yankin.
Dalilin matasa na goyon bayan Ali Ndume
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa matasan sun bayyana cewa wannan mataki wata hanya ce ta tabbatar da ci gaba da wakilci daga wanda suka kira jarumin dan majalisa mai kishin jama’a.
Mai kula da shirye-shiryen matasa, Alhaji Babandi Shehu, ya ce wannan ba kawai tara kudin siyasa ba ne, illa wata sanarwa ce mai ma’ana a lokacin da kasar ke bukatar jaruman shugabanni.
Ya ce:
"Sanata Ndume na daga cikin ‘yan siyasar da ke fada wa gwamnati gaskiya a kai a kai. Wannan ba batun kudin fam kadai ba ne, batun kare wakilci ne da ke fifita muradun jama’a tare da tunatar da ɓangaren zartarwa.”
Matasa sun amince da wakilcin Ndume
Sun jaddada cewa ayyukansa a majalisa da kuma cigaban mazaba sun tabbatar da cancantarsa na ya ci gaba da zama yana wakiltarsu.
Babban mai taimaka masa a majalisa, Junaid Jibril Maiva, ya bayyana cewa Sanata Ndume ya shafe sama da shekaru goma yana bayar da gudunmawa mai tasiri.
Ya ce ya dauki nauyin sama da kudirori 70 da suka shafi ci gaban kasa, tare da samar da muhimman cibiyoyin gwamnati a Kudancin Borno da yankin Arewa maso Gabas baki daya.

Source: Facebook
Daga cikin ayyukan da aka ambata akwai jami’ar sojojin Najeriya da ke Biu, hukumar raya Arewa maso Gabas, da Kwalejin Ilimi ta tarayya da ke Gwoza.
Haka kuma ana kokarin kafa cibiyar kiwon lafiya ta tarayya a Kwaya-Kusar da Kwalejin Noma a Shani. Maiva ya kara da cewa Sanatan ya taka rawa wajen taimakon jin kai, musamman a yankunan da rikicin ta’addanci ya shafa.
Ali Ndume ya caccaki Tinubu
A baya, mun wallafa cewa Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume ya sake caccakar hadiman shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu kan halin da kasa ke ciki.
Ndume ya bayyana cewa Tinubu ya zagaye kansa da wadanda ba su san siyasa ba, shi yasa bai san halin da 'yan Najeriya ke ciki ba ganin irin wahalar da ake ciki.
Ɗan majalisar dattawan ya yi gargadin cewa matukar Bola Ahmed Tinubu bai dauki matakin gyara ba, to hakan zai shafi sakamakon zabe mai zuwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

