Muhimman Abubuwa 4 da Jam'iyyun Adawa Suka Yi Matsaya gabanin Zaben 2027

Muhimman Abubuwa 4 da Jam'iyyun Adawa Suka Yi Matsaya gabanin Zaben 2027

Ibadan, Oyo State - A karshen makon da ya gabata ne 'yan adawar Najeriya suka gudanar da wani taro a birnin Ibadan na jihar Oyo a wani mataki na kulla hadaka gabanin 2027.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Wakilan jam'iyyun fiye da 10 sun halarci wannan taro, wanda suka shirya domin hada karfi da karfe da nufin kwace mulki daga hannun shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da jam'iyyarsa ta APC.

Taron Ibadan
Gwamna Seyi Makinde, Atiku Abubakar da manyan jiga-jigan adawa a taron da suka gudanar a Ibadan Hoto: Adeniyi Rotimi Johnson
Source: Facebook

Jiga-jigan adawa sun hadu a Ibadan

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar na cikin manyan jiga-jigan da suka halarci wannan taro kamar yadda ya tabbatar a shafinsa na Facebook.

Tsofaffin yan takarar shugaban kasa, Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi, tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, Gwamna Seyi Makinde, sanatoci da yan Majalisar tarayya na jam'iyyun adawa sun halarci wannan taro.

Kara karanta wannan

2027: Shettima ya yi gargadi kan rusa APC bayan zaben fitar da gwani

Jam'iyyun adawa da suka halarci taron

Haka nan kuma jam'iyyun adawa da suka halarci taron sun hada da ADC, PDP, LP, NNPP, PRP, Accord, APM, YP, ADP, da sauran makamantansu.

A taron dai manyam jam'iyyun adawa kamar ADC, NNPP da PDP sun nuna cewa abu ne mai wahala a iya kayar da Shugaba Tinubu matukar tsagin adawa ba su dunkule wuri guda ba.

Bisa haka ne yan adawar suka yi nazari tare da cimma matsaya kan muhimman batutuwa da suka shafi zaben 2027 wanda ke kara kusantowa.

Muhimman abubuwan da suka yi matsaya

Legit Hausa ta tattaro muku muhimman abubuwa hudu da jagororin adawar Najeriya suka cimma matsaya a wannan tafo domin tunkarar zaben 2027.

1. Tsaida dan takarar shugaban kasa 1

Yayin taron, manyan jam'iyyun adawa, PDP, LP, ADC da NNPP sun bada shawarar hada kai gaba daya domin tunkarar zaben 2027.

Vanguard ta ruwaito cewa sakamakon haka, jam'iyyun da suka halarci taron suka cimma matsayar cewa za su dunkule wuri guda, su fitar da dan takarar shugaban kasa guda daya, kuma su mara masa baya don ceto kasa.

Kara karanta wannan

Bayan an yi masa tayin takara, shugabannin NDC sun gana da Kwankwaso a gidansa

2. Bukatar cire shugaban INEC

Wani abu da jam'iyyun adawar suka amince da shi, shi ne batun shugaban hukumar zabe mai zaman kanta da kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan.

'Yan adawar sun yanke shawarar cewa za su ci gaba da matsa wa gwamnati lamba da kiraye-kirayen sauya shugaban INEC domin a cewarsu, ta haka ne za a shirya sahihin zabe, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

Tun bayan nada Farfesa Amuptan ya fara shan suka daga bangarori daban-daban ciki har da jam'iyyun adawa kamar ADC, inda suka bukaci ya yi murabus daga mukamin.

Taron yan adawa.
Tsofaffin yan takarar shugaban kasa, Rabiu Kwankwaso da Peter Obi tare da jama'a a taron jam'iyyun adawa a Ibadan Hoto: Adeniyi Rotimi Johnson
Source: Facebook

Jam'iyyun adawa sun zargi Amupitan da nuna son kai da goyon baya ga jam'iyyar APC mai mulki, shi yasa suke ganin bai kamata ya jagoranci shirya zaɓen gama-gari na 2027 ba.

3. Sake gyara dokar zaben Najeriya

Bugu da kari, 'yan adawar sun tattauna kan dokar zabe ta 2026 wacce Majalisar tarayya ta 10 ta yi wa garambawul a watannin da suka wuce.

Kara karanta wannan

Emefiele: An ji yadda aka yi amfani da sa hannun Buhari aka cire makudan kudi a bankin CBN

A taron da suka gudanar, hadakar jam'iyyun adawa sun amince cewa za su ci gaba da kiraye-kiraye domin Majalisar ta sake gyara wannan doka da suke ganin barazana ce ga zabe.

Sun ce ya zama dole Majalisa ta cire dukkan sassan da ke barazana ga sahihancin zaɓe, kuma waɗanda suka saɓa da tanade-tanaden kundin tsarin mulki, in ji rahoton BBC Hausa.

4. Gyara jadawalin zaben 2027

Haka zalika, jam'iyyun adawa zama da 10 da suka halarci wannan taro sun nuna damuwarsa kan wasu kayyadaddun lokuta da gindaya a jadawalin zaben 2027 musammn wa'adin tsaida yan takara.

Sun bayyana cewa sun dauki ƙa'idojin da INEC ta fitar a jadawalin a matsayin cikas, waɗanda aka tsara da gangan domin ƙaƙaba wa jam'iyyun adawa sharudda da wa'adin lokaci.

Don haka suka jaddada cewa suna buƙatar INEC ta tsawaita wa'adin gudanar da zaɓen fitar da gwani har zuwa ƙarshen watan Yuli, 2026, kamar yadda Tribune Online ta kawo.

Taron adawa.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, shugaban tsagin PDP, Tanimu Tura ki da shugaban ADC, David Mark a taron Ibadan Hoto: Adeniyi Rotimi Johnson
Source: Facebook

INEC ta maida sunayen shugabannin ADC

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sabunta bayanan shafinta na yanar gizo, biyo bayan hukuncin Kotun Koli kan shugabancin jam'iyyar ADC.

Kara karanta wannan

2027: An kunna rikici a PRP da ke shirin kawar da Tinubu, ADC ta magantu

Hukumar INEC ta maida sunayen Sanata David Mark a matsayin shugaban jam’iyyar ADC na kasa da Rauf Aregbesola a matsayin sakataren jam'iyyar hadaka.

Wannan ci gaba ya soke matakin da INEC ta ɗauka a farkon watan Afrilu na cire shugabancin da Mark ke jagoranta daga shafinta, inda ta dogara da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262