Miyagun Kwayoyi: Dubun Tsohon Shugaban Karamar Hukuma Ta Cika, An Cafke Shi a Kano
- An kama tsohon shugaban ƙaramar hukumar Rogo ta Kano kan zargin sayar da allurar fenta ga matasa ta haramtacciyar hanya
- Kwamitin hadin gwiwa ya ce wani matashi ya gano tsohon shugaban a matsayin wanda ke samar masa da ƙwayar
- Ana zargin wanda ake tuhumar da gudanar da aikin jinya ba tare da lasisin aikin jinya ba tun shekarar 1985
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Kwamitin Jihar Kano kan Miyagun Ƙwayoyi da Laifukan da suka Shafi Hakan ya kama tsohon shugaban ƙaramar hukumar Rogo bisa zargin sayarwa da yi wa matasa allurar fenta.
Shugaban kwamitin, Muhuyi Magaji Rimingado, ne ya bayyana kamen a wata hira ta bidiyo da wata kafar yaɗa labarai ta cikin gida ranar Litinin.

Source: Facebook
A rahoton da Daily Trust ta wallafa, ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan wani samame na ɓoye ya tabbatar da zargin cewa yana samar da wannan allura mai matuƙar haɗari.
Sai dai Muhuyi Rimingado bai bayyana sunan tsohon shugaban ƙaramar hukumar ba.
Yadda aka kama tsohon ciyaman
Rimingado ya ce binciken ya fara ne bayan kwamitin ya kama wani matashi wanda hannunsa ya lalace sosai sakamakon yawan yi masa allurar.
Daga baya, wanda lamarin ya shafa ya bayyana tsohon shugaban ƙaramar hukumar a matsayin wanda ke samar masa da miyagun ƙwayoyin.
“Jami’anmu sun bi wanda lamarin ya shafa zuwa wurin wanda ake zargin. Ya ba shi kuɗi kuma aka gaya masa ya dawo daga baya.
"Da ya dawo, wanda ake zargin ya ɓoye allurar a cikin ambulan. Yana dab da miƙa masa ita ne jami’anmu suka kutsa suka kama shi,” in ji Rimingado.
Ya ƙara da cewa wanda ake zargin ya fara musanta hannu kai tsaye a lamarin, yana cewa ana kawo irin wadannan ƙwayoyin ne daga Kasuwar Sabon Gari.
An gano ƙarin hujjoji
Sai dai kwamitin ya ce ya samu isassun hujjoji da suka haɗa da ƙwayar da aka samu a hannun wanda ake zargin, shaidar wanda lamarin ya shafa da kuma bayanin da wanda ake zargin da kansa ya bayar.

Kara karanta wannan
Tinubu ya tsallake kansa, Buhari da Yar'adua, ya faɗi shugaban da ya fi amfanar Najeriya
Kwamitin ya kuma bayyana cewa an rufe cibiyar lafiya ta tsohon shugaban karamar hukumar bayan hukumomi sun tabbatar da cewa ba ta da cikakken lasisi.
Rimingado ya zargi tsohon ciyaman sin da yin aikin jinya ba tare da ingantaccen lasisin aikin jinya ba tun daga shekarar 1985.

Source: Original
An gurfanar da shi a gaban kotu
A cewar Rimingado, an gurfanar da wanda ake zargin ƙarƙashin Sashe na 249 na Kundin Laifuffuka na Jihar Kano, wanda ya shafi laifukan da suka shafi amfani da abubuwa masu cutarwa.
Shugaban kwamitin ya jaddada cewa kwamitin zai gabatar da kwararan hujjoji a gaban kotu, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
Za a shirya taro kan shaye-shaye a Kano
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Kano za ta hada gwiwa da Kwamitin Majalisar Wakilai wajen shirya taron yaki da shaye-shaye da safarar miyagun kwayoyi.
Taron zai hada masu tsara manufofi, jami'an tsaro, kwararrun ma'aikatan lafiya, sarakunan gargajiya, shugabannin addini, kungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki.
Asali: Legit.ng
