Matatar Man Dangote Ta Shiga Kasuwar Hannun Jari da Kafar Dama, An Zuba $1bn

Matatar Man Dangote Ta Shiga Kasuwar Hannun Jari da Kafar Dama, An Zuba $1bn

  • Matatar man Dangote ta samu tsarin bayar da tabbacin zuba jarin $1bn domin tallafa wa shirin sayar da hannun jarin kamfanin ga jama’a
  • Daga cikin kudin akwai dala miliyan 600 da aka riga aka kammala zuba jarinsu, yayin da aka ware karin Dala miliyan 400 habaka tsarin
  • Alhaji Aliko Dangote ya ce yarjejeniyar wani muhimmin mataki ne ga matatar da kuma kasuwannin hada-hadar hannayen jari na Afrika

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos – Matatar Man Fetur ta Dangote ta samu tabbacin zuba jarin $1bn gabanin shirin sayar da wani kaso na hannun jarinta ga jama’a.

Kamfanonin Marob Strategies and Consulting DIFC Ltd da Lilium Capital ne suka tsara tsarin, wanda ya kunshi Dala miliyan 600 na zuba jari na kashin kai da aka riga aka kammala.

Kara karanta wannan

Abin kunya: An kama matashin da ya shiga gida satar ɗan kamfan matar aure

Likkafar matatar Dangote ta daga
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote Hoto; Bloomberg
Source: Getty Images

Jaridar Tha Cable ta wallafa cewa haka kuma an samu karin Dala miliyan 400 da aka yi alkawarin samarwa domin tallafa wa shirin sayar da hannun jarin matatar.

An fara shirin hannun jarin Dangote

Jaridar Punch ta kawo labarin cewa a cikin wata sanarwa da Dangote ya fitar ranar Talata, 18 ga watan Agusta, 2026, kamfanin ya ce Pan-African Refinery Investment SPV, wani reshe na Lilium Capital Group, ne ya samar da kuma tabbatar da Dala miliyan 600 da aka zuba a matatar.

Kamfanin ya kara da cewa Marob Strategies da Lilium Capital yanzu suna jagorantar rabon damar zuba jarin a tsakanin masu zuba jari daga sassa daban-daban na Afrika.

Kamfanin ta kara da cewa ana tuntubar asusun ajiyar gwamnati, gwamnatoci, manyan masu zuba jari da sauran wadanda suka cancanci shiga harkar.

Ana sa ran zuba jari a matatar Dangote

A cewar masu ba da shawarar kan yarjejeniyar, an samu wadanda suka nuna sha’awar zuba jari, wanda ke nuna cewa ana bukatar irin wadannan manyan ayyuka a Afrika.

Kara karanta wannan

Sojoji sun ɗana tarko, an daƙile harin garkuwa da mutane a Zamfara

Ana shirin fara sayar da hannun jarin matatar ga yan kasuwa
Wata motar kamfanin Dangote Hoto: Dangote Industries
Source: Facebook

Ana kuma sa ran shirin zai taimaka wajen kara yawan shuge da ficen jari tsakanin kasashen Afrika tare da bude hanya ga samun kasuwar hada-hadar jari shiyyar.

Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana yarjejeniyar a matsayin wani muhimmin mataki ga matatar da kasuwannin hada-hadar jari na Afirka.

Ya ce yarjejeniyar ta nuna yadda masu zuba jari ke da yakinin muhimmancin matatar a fannin dabarun tattalin arziki, tare da samar da damar da asusun ajiyar gwamnati.

Matatar Dangote ta kafa tarihi

A wani labarin, kun ji cewa matatar hamshakin dan kasuwa kuma attajiri lamba daya a Afrika, Aliko Dangote ta sake kafa tahiri wajen jigilar man jirgi zuwa nahiyar Turai.

Alkaluma sun nuna cewa matatar Dangote ta zarce Amurka, ta zama babbar mai samar da man jiragen sama ga Turai karo na biyu a jere bayan fara yakin Gabas ta Tsakiya.

Rahoton kamfanin Kpler ya nuna matatar ta fitar da tan sama da 400,000 na jet fuel zuwa Turai a watan Yulin 2026 lamarin da ya kara daga darajar Najeriya a fannin makamshi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng