Atiku, Kwankwaso da Sauran 'Yan Adawa Sun Cimma Matsayar da Za Ta Girgiza Tinubu a 2027
- Jam'iyyun adawa sun gudanar da babban taro a birnin Ibadan domin tattauna batutuwan da suka shafi siyasar kasar nan
- Babban taron ya samu halartar manyan jiga-jigai da suka hada da Atiku Abubakar, Rabiu Musa Kwankwaso da sauransu
- A wurin taron, sun amince da yadda za su fitar da dan takara domin fafatawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Ibadan, jihar Oyo - Jam’iyyun adawa sun sanar da shirinsu na fafatawa da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben shekarar 2027.
Jam'iyyun adawar sun bayyana shirinsu na gabatar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya tilo domin zaɓen shekarar 2027.

Source: Twitter
Jaridar The Cable ta kawo rahoton cewa jam'iyyun adawar sun amince da wannan matsayar ne a ranar Asabar, 25 ga watan Afirilun 2026.
'Yan adawa sun yi taro a Ibadan
An cimma matsayar ne yayin babban taron shugabannin jam’iyyun adawa na ƙasa da aka gudanar a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Jaridar Vanguard ta ce an bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da aka fitar bayan babban taron da jam'iyyun adawar suka gudanar.
Manyan jiga-jigan adawa da suka haɗa da Atiku Abubakar, Rabiu Musa Kwankwaso, Rotimi Amaechi, Peter Obi da Rauf Aregbesola, sun halarci taron.
'Yan adawa za su yaki Tinubu da APC
Yayin da yake karanta sanarwar bayan taron, shugaban ɓangaren jam’iyyar PDP, Taminu Turaki, ya ce bayyana cewa:
“Za mu bijire wa duk wata makirci na APC na son mayar da Najeriya ƙasa mai jam’iyya ɗaya tilo, kuma za mu yi yaƙi domin dorewar tsarin dimokuraɗiyya mai jam’iyyu da dama a ƙasarmu.”
Game da zaɓen 2027, ‘yan adawar sun yi watsi da iƙirarin cewa an riga an san sakamakon zaɓen, inda suka bayyana cewa:
“Duk da dabarun jam’iyya mai mulki, za mu fitar da ’yan takara kuma mu fafata a zaɓen shugaban ƙasa da sauran zaɓukan 2027.”
An cimma matsaya kan fitar da dan takara
Jam’iyyun adawar sun kuma bayyana shirinsu na tsayawa takara a ƙarƙashin inuwa ɗaya, inda suka ce:
"Za mu yi aiki wajen fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya na zaɓen 2027, wanda dukkan jam’iyyun adawa da ke halartar taron za su amince da shi tare da ba shi goyon baya domin ceto al’ummarmu da suka daɗe suna shan wahala.”

Source: Twitter
Dangane da fargaba game da hukumar zaɓen, sanarwar ta bayyana cewa:
“Shugaban hukumar INEC, Joash Ojo Amupitan, tun da ya nuna son zuciya da nuna goyon baya ga jam’iyyar APC mai mulki, bai kamata ya gudanar da babban zaɓen 2027 ba.”
Sun soki tsare jiga-jigan 'yan adawa
Haka kuma sanarwar ta taɓo batun zargin danne haƙƙin siyasa, inda ta ce:
“Dukkan manyan ’yan siyasa da ake tsare da su ko ake muzantawa kan laifuffukan da za a iya bayar da belinsu, a sake su nan take kuma a ba su damar amfani da haƙƙinsu na ’yan ƙasa wajen shiga harkokin siyasa ba tare da nuna bambanci ba.”
Atiku Abubakar ya soki dokar zabe
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya soki wani sashe na dokar zabe da aka amince da ita.
Atiku Abubakar ya soki wani sashe na dokar zabe da ke bai wa jami’in tattara sakamako damar kirga takardun kuri'a da ba su da hatimin INEC.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce wannan matsala na iya zama barazana ga sahihancin zabubbukan Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


