Emefiele: An Ji Yadda Aka Yi Amfani da Sa Hannun Buhari Aka Cire Makudan Kudi a Bankin CBN

Emefiele: An Ji Yadda Aka Yi Amfani da Sa Hannun Buhari Aka Cire Makudan Kudi a Bankin CBN

  • Wani shaidan EFCC ya fallasa yadda aka yi amfani sa hannun tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari na bogi wajen cire kudi a CBN
  • Chinedu Eneanya, wanda jami'i ne a EFCC ya ce bincike ya nuna yadda aka fitar da Dala miliyan 6.23 a lokacin tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele
  • Ya kara da cewa an samo takardun da suka ba da izinin fitar da kudin daga bankin, sannan an yi tambayoyi ga mutanen da ke da hannu a lamarin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta'adi (EFCC) ta ci gaba da gabatar da shaidu a shari'ar tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.

Wani shaida da aka gabatar a gaban kotun babban birnin Tarayya Abuja, ya bayyana cewa an cire Dala miliyan 6.23 daga CBN da sunan aikin sa ido kan zaben 2023 a lokacin mulkin Emefiele.

Kara karanta wannan

Matakan da gwamnati ta dauka da aka samu bullar annobar COVID 19 a Najeriya

Emefiele.
Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele Hoto: @CentBank
Source: Getty Images

Yadda aka cire $6.23m daga bankin CBN

The Cable ta ce shaidar, Chinedu Eneanya, wanda jami'i ne a EFCC, ya ce binciken su ya gano cewa an fitar da kudaden daga asusun CBN da nufin biyan masu sa ido kan zaben Najeriya na kasashen waje.

“Bincike ya nuna cewa an cire Dala miliyan 6.23 daga CBN domin wai a biya masu sa ido na kasashen waje a zaben 2023,” in ji shi.

Ya kara da cewa an samo takardun da suka ba da izinin fitar da kudin daga bankin, sannan an yi tambayoyi ga mutanen da ke da hannu a lamarin.

Zarge-zargen da ake yi wa Emefiele

EFCC na tuhumar Emefiele da laifuffuka 20 da suka hada da cin amana, kirkirar takardu na bogi, damfara, zamba a harkar sayayya da kuma hadin baki.

Hukumar ta ce an biya kudin ne bisa wani shiri na bogi na masu sa ido kan zabe, sai dai Emefiele ya musanta dukkan tuhume-tuhumen.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama wani mai taimaka wa 'yan ta'adda a filin jirgin sama a jihar Yobe

An yi amfani da sa hannun Buhari na bogi

Shaidar ta ce binciken fasaha ya nuna cewa an yi amfani sa hannun tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha na bogi domin a fitar da kudin.

Shari’ar tsohon gwamnan CBN na ci gaba da daukar sabon salo bayan masu gabatar da kara sun kasa kawo karin shaidu duk da shirye-shiryen bangaren wanda ake tuhuma.

Sai dai bangaren tsohon gwamnan bankin CBN ya bukaci kotu ta rufe karbar shaidu daga wakilan gwamnati idan suka ci gaba da yin jinkiri.

Kotu.
Gudumar da alkalai ke amfani da ita a kotu Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Kotu ta dage zaman shari'ar Emefiele

Alkalin kotun, Hamza Mu’azu, ya umurci bangarorin biyu su ajiye hujjojinsu har zuwa rubutaccen jawabi na karshe, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Ya kuma umarci masu kara su hada kai da rajistar kotu domin fitar da sammaci ga shaidun, sannan ya dage sauraron karar zuwa ranar Talata mai zuwa.

An kara taso Emefiele a gaban kotu

Kara karanta wannan

2027: An fara zargin Obi zai yaudari 'yan Arewa saboda ya muzguna masu a baya

A wani labarin, kun ji cewa wani shaida a kotu ya bayyana cewa yadda tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya rubuta takarda domin neman amincewa Buhari kan sake fasalin kudi.

A cewar shaidar da EFCC ta gabatar, marigayi Muhammadu Buhari ya amince da shirin ne da sharadin a rika buga sababbin kudin a cikin gida

Ya shaida wa kotu cewa kamfanin De La Rue na Birtaniya ne ya tsara zanen kudin, yayin da Kamfanin Buga Kudi na Najeriya (NSPM) ya dauki nauyin buga kudaden, lamarin da ya saba wa umarnin Buhari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262