Abin da ADC Ta Yi Wanda Ya Taimaka wajen Kayar da Jam'iyyar APC a Zaben Gwamnan Osun
- Sakataren yaɗa labarai na ADC, Bolaji Abdullahi, ya ce jam’iyyarsu ta yi aiki tare da Accord domin hana APC samun nasara a zaɓen gwamnan Osun
- Abdullahi ya ce kayar da APC ita ce babbar nasara ga ADC duk da cewa ɗan takararsu ya samu ƙuri’u 17,180 kacal
- Ya ce haɗin kan jam’iyyun adawa na iya ba su damar kayar da APC a zaɓen shugaban ƙasa na 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Osun, Nigeria - Jam'iyyar ADC ta yi ikirarin cewa ta yi hadin gwiwa da jam'iyyar Accord domin hana APC samun nasara a zaben gwamnan jihar Osun na 2026.
Sakataren yaɗa labaran ADC na kasa, Bolaji Abdullahi, ya ce jam’iyyarsu ta yi aiki tre da gwiwa da Accord a zaɓen gwamnan jihar Osun, kuma sun yi nasarar dakile yunkurin APC na karbe mulki.

Source: Facebook
ADC ta hada kai da Accord a Osun
Abdullahi ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Trust TV ranar Litinin, yayin da yake tsokaci kan yadda ADC ta yi a zaɓen da aka gudanar ranar 15 ga Agusta, 2026.
Ɗan takarar ADC a zaɓen, Najeem Salaam, ya samu ƙuri’u 17,180, wanda ya ba shi damar zama na uku.
Gwamnan jihar mai ci kuma ɗan takarar Accord, Ademola Adeleke, ya samu ƙuri’u 511,067, inda ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Bola Oyebamiji na APC, wanda ya samu ƙuri’u 444,815.
Kayar da APC ita ce nasara ga ADC
Abdullahi ya ce jam’iyyar ta yi hasashen cewa rabuwar ƙuri’un ‘yan adawa na iya bai wa APC damar samun nasara.
Kakakin ADC ya ce:
"Mun ga yiwuwar haɗin gwiwa saboda mun fahimta tun da wuri cewa idan muka tafi ba tare da hada kai ba, akwai yiwuwar ƙuri’un adawa su rabu, APC kuma ta samu nasara. Shi ya sa muka ga damar yin aiki tare, kuma abin da muka yi kenan.”
Abdullahi ya ce ADC ba ta ɗauki ƙarancin ƙuri’un da ɗan takararta ya samu a matsayin rashin nasara ba, saboda babban abin da jam’iyyar ta sa a gaba shi ne hana APC komawa mulki a jihar, cewar rahoton The Cable.

Source: Twitter
“Shi ya sa za mu iya murnar abin da ya faru a Osun cikin kwarin gwiwa, domin a wajenmu, nasara na nufin an kayar da APC."
“Saboda haka, ba mu ɗauki rashin nasarar ɗan takararmu na gwamna a matsayin rashin nasara ko gazawa ba. Kayar da APC ita ce ainihin nasara a gare mu,"
- Bolaji Abdullahi.
Atiku ya gamsu da zaben gwamnan Osun
A wani labarin, kun ji cewa Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma dan takarar ADC a zaben 2027, Atiku Abubakar ya bayyana gamsuwa da zaben gwamnan Osun.
Atiku ya taya Gwamnan Osun, Ademola Adeleke , murnar sake lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar a jiya Asabar 15 ga watan Agustan 2026.
Ya yaba wa hukumar INEC kan tabbatar da zabe sahihi wanda zai iya zama zakaran gwajin dafi a babban zaben shekarar 2027 da ake tunkara.
Asali: Legit.ng

