An Buga Gangar Siyasar 2027: INEC Ta ba Jam’iyyu Wa'adin Fitar da 'Yan Takara

An Buga Gangar Siyasar 2027: INEC Ta ba Jam’iyyu Wa'adin Fitar da 'Yan Takara

  • Hukumar INEC ta sanar da fara shirin babban zaɓen 2027, inda ta ba jam’iyyu wa'adin ranar 23 ga Afrilu zuwa 30 ga Mayu, 2026, domin fitar da ƴan takara
  • Dole ne jam'iyyun siyasa su miƙa jerin sunayen mambobinsu ga hukumar INEC aƙalla kwanaki 21 kafin gudanar da zaɓen fitar da gwani
  • Yayin da ƴan Najeriya ke bayyana ra'ayoyi daban-daban game da wannan lokaci, INEC ta jaddada buƙatar gudanar da zaɓukan cikin gaskiya da adalci

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja – Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta buga gangar ayyukan babban zaɓen shekarar 2027 a hukumance.

INEC ta bude labulen fara shirin zabukan ne ta ta hanyar bada wa'adin kwanaki 38 ga jam'iyyun siyasa domin gudanar da zaɓukan fitar da gwani.

INEC ta ba jam'iyyu wa'adin gudanar da zabukan fitar da gwani
Shugaban INEC, Prof. Joash Amupitan, ya na jawabi a taron masu ruwa da tsaki a ofishin hukumar, Abuja. Hoto: @inecnigeria
Source: Twitter

2027: Hukumar INEC ta ba jam'iyyu wa'adi

Kara karanta wannan

Sabon salo: APC ta faɗi tsari 2 da za ta yi amfani da su wajen zaɓen ƴan takara

Wannan tsari, wanda ya fara a yau 23 ga Afrilu, zai ci gaba har zuwa ranar 30 ga Mayu, 2026, kamar yadda rahoton PM News ya nuna.

Wa'adin ya shafi zaben fitar da gwani na kujerar shugaban kasa, gwamnoni, 'yan majalisar tarayya (sanatoci da majalisar wakilai) da 'yan majalisar jihohi.

Hukumar INEC ta bayyana cewa wannan lokaci zai ba jam'iyyu damar magance duk wata takaddama da ka iya tasowa sakamakon zaɓukan cikin gida.

Sharruɗan INEC ga jam’iyyun siyasa

A ƙarƙashin sababbin matakan hukumar, an tilas wa dukkan jam'iyyun siyasa 18 da za su shiga zaben su miƙa kundin mambobinsu ga INEC aƙalla kwanaki 21 kafin ranar zaɓen fitar da gwani.

INEC ta sanya ranar 10 ga Mayu, 2026, a matsayin ranar ƙarshe ta miƙa waɗannan takardu.

Hukumar ta yi kira ga masu ruwa da tsaki da su tabbatar an gudanar da zaɓukan cikin gaskiya da adalci, tare da kauce wa duk wani abu da zai kai su ga fuskantar matsalolin shari'a a nan gaba.

Yadda 'yan Najeriya ke maida martani

Tuni dai ƴan Najeriya suka fara tofa albarkacin bakinsu game da wannan mataki na INEC, kamar yadda Legit Hausa ta gani a labarin da hadimin shugaban jam'iyyar APC, Imran Muhammad ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun kutsa asibiti a Neja, babban likita ya fada hannun miyagu

INEC ta bukaci jam'iyyun siyasa su gudanar da zabukan fitar da gwani cikin adalci
Jami'an hukumar INEC na tantance masu kada kuri'a. Hoto: @inecnigeria
Source: Twitter

Yayin da wasu ke kallon hakan a matsayin farkon "kakar wasan siyasa," wasu kuma na nuna damuwa kan yanayin lokacin da aka bada don gudanar da zaben.

Taiwo Adeniyi:

"Dole ne a mika rajista kafin ranar 10 ga watan Mayu. Don Allah a gaya wa 'shugaban intanet' da masoyansa su fara rubutu tun yanzu, domin kada su zargi INEC da gazawar fasaha a shekarar 2027. Mu muna shirye, ku fa?"

Chris:

"Kwanaki 38 na zabukan fitar da gwani? Amma ina son sani; ya muke ji game da fara wannan shiri alhalin wasu kararraki har yanzu suna gaban Kotun Koli? Shin lokacin ya dace, ko kuwa muna gaggawar shiga wani sabon zaben ne ba tare da mun gyara barakar baya ba?"

Godwin Ubi:

"Anan ne za mu gane ko ADC ta san harkar siyasa ko ba ta sani ba. Idan ba za su iya tunkarar wannan karamin kalubale da ke gabansu ba, to akwai damuwa idan har za mu amince musu da manyan batutuwan da suka shafi Najeriya."

Kara karanta wannan

Kisan Kiristoci: Sanatan Amurka ya tona asirin wasu jami'an gwamnatin Najeriya

Duba martanin jama'a a kasa:

APC ta dage zaben fitar da gwani

A wani labari, mun ruwaito cewa, jam'iyyar APC ta dage gudanar da zaben fitar da gwani da ta shirya gudanarwa a ranar 15 da 16 ga Mayu zuwa 23 ga Mayu 2026.

A yanzu, APC ta mayar da lokacin gudanar da zaben fitar da gwaninta zuwa 21 ga Mayu, 2026, wanda ya yi dai-dai da sabon jadawalin zabukan 2027 da INEC ta fitar.

Mataimakin sakataren watsa labaran jam'iyyar na kasa, Duro Meseko ne ya sanar da hakan a karshen taron kwamitin NWC na jam'iyyar karo na 186 da aka gudanar a Abuja.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com