Atiku Ya Tono 'Babbar Matsala' kan Kada Kuri'a a 2027, Ya Ce za a Yi Magudi

Atiku Ya Tono 'Babbar Matsala' kan Kada Kuri'a a 2027, Ya Ce za a Yi Magudi

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya caccaki dokar da aka yi game da kirga takardun kada kuri'a ko ba su da alamar INEC
  • Hakan na zuwa ne yayin da jam'iyyun siyasa ke kara shiri game da zaben 2027, inda ya ce dokar za ta bude kofa ga yin magudin zabe
  • Atiku Abubakar ya yi kira ga majalisar tarayya da ta gaggauta daukar mataki game da dokar kafin a kai lokutan kada kuri'a a zabe mai zuwa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya soki wani sashe na dokar zabe da ke bai wa jami’in tattara sakamako damar kirga takardun kuri'a da ba su da hatimin INEC.

Ya ce wannan matsala na iya barazana ga sahihancin zabukan Najeriya, yana mai jaddada cewa ba karamar matsala ba ce.

Kara karanta wannan

2027: Kano da wasu jihohin Arewa 7 da majalisa ke son haramta wa yin kamfen

Atiku Abubakar a gidan shi da ke Abuja
Atiku Abubakar yayin ganawa da baki a Abuja. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

The Cable ta wallafa cewa Mai ba shi shawara kan hulda da jama’a, Phrank Shaibu ya ce Atiku ya bayyana sashe na 63 na dokar a matsayin babban kuskure mai hadari.

Gargadin Atiku Abubakar kan dokar zabe

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi gargadi da cewa duk wata doka da za shafi tattara kuri'u za ta iya zama wata kafa da za a iya amfani da ita wajen karkatar da muradin jama’a.

“Wannan ba karamar matsala ba ce, barazana ce kai tsaye ga ingancin zabe,”

In ji sanarwar.

“Dimokuradiyya ba za ta iya tsayuwa a kan rashin tabbas ba. Dole ne takardun kada kuri'a su cika sharuda.
“Za a bude kofar magudi, rikici da kuma rudani.”

Karin bayanin Atiku kan dokar zabe

Atiku ya ce duk da cewa an kafa wannan tanadin doka ne don hana tauye hakkin masu kada kuri’a, yadda yake a yanzu na iya raunana amincewar jama’a da tsarin zabe.

Kara karanta wannan

Trump ya fitar da sanarwa yayin da wa'adin tsagaita wuta da Iran zai kare

“A lokacin da ‘yan Najeriya ke bukatar gaskiya da sahihanci, abu ne mai hadari a bar wani sashe da ke rage kwarin gwiwa a ginshikin dimokuradiyya, wato kuri’a,”

In ji shi

Yadda wani mutum ke kada kuri'a yayin zabe
Wani mutum na kada kuri'a a zaben Abuja na 2026. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Kiran Atiku ga Majalisar tarayya

Atiku ya bukaci majalisar dokokin kasa da ta gyara dokar domin kawar da duk wata damar kawo son rai wajen tantance takardun zabe, tare da kafa tsauraran ka’idoji da za su kare ingancin kowace kuri’a.

“Ya kamata shugabannin majalisar dokoki su kasance masu taka-tsantsan wajen kula da irin wadannan sashe da ke shafar dimokuradiyyarmu,”

in ji shi.

Punch ta wallafa cewa ya kara da cewa:

“Takardun zabe kayan aiki ne na doka wanda sahihancinsu ke da matukar muhimmanci ga amincewar dukkan tsarin zabe.”

Jonathan ya yi wa Atiku raddi

A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya yi wa Atiku Abubakar raddi kan caccakar shi da ya yi.

Atiku Abubakar ya yi kakkausar suka ga salon mulkin shugaba Jonathan, inda ya bayyana cewa ya gaza a wasu bangarori da dama.

Sai dai Jonathan ya nuna cewa kowa na iya yin kuskure a kan mulki amma ya yi iya kokarinsa wajen kawo gyara a lokacinsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng