Mark da Nafi'u Gombe: Kotun Koli Ta Yanke Hukunci kan Rikicin Shugabancin ADC
- Kotun Koli ta tabbatar da tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Mark a matsayin shugaban ADC na kasa
- Kwamitin alkalai biyar karkashin jagorancin Mai Shari'a Mohammed Lawal Garba ya soke umarnin kotun daukaka kara na a tsaya inda ake
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya yi maraba da wannan hukunci, yana mai cewa akwai sauran aiki a gaba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Kotun Kolin Najeriya ta yanke hukunci a karar da shigar gabanta game da rikicin shugabanci da ya addabi jam'iyyar yan hamayya ta ADC.
Kotun mai daraja ta daya a kasar nan ta tabbatar da tsohon shugaban Majalisar dattawa, Sanata David Mark a matsayin halastaccen shugaban jam'iyyar ADC ta kasa.

Source: Twitter
Kwamitin alkalai biyar da ya saurari shari'ar rikicin ADC ne ya yanke wannan hukuncin a yau Alhamis, 30 ga watan Afrilu, 2026, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Kotun koli ta ba David Mark gaskiya
A hukuncin da alkalan suka yanke, Kotun koli ta soke umarnin “kowa ya tsaya a matsayinsa” da Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta bayar kan rikicin shugabancin ADC.
Wannan hukunci ya dawo da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar karkashin jagorancin David Mark, bayan da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta cire su daga shafinta.
Alkalai biyar karkashin jagorancin Mohammed Lawal Garba sun ce umarnin da kotun daukaka kara ta bayar ba shi da muhimmanci.
Shari'a za ta koma babbar kotun tarayya
Bayan haka, Kotun Koli ta umarci msu karar da du koma babbar kotun tarayya domin ci gaba da shari'ar da suka yi.
Tun da farko dai tsohon mataimakin shugaban ADC na ƙasa (Arewa), Nafi'u Bala Gombe ne ya shigar da tsagin David Mark ƙara a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, yana zargin su da ƙwace masu jam'iyya.
Bisa umarnin kotun koli, bangarorin za su koma kotun tarayya don ci gaba da wannan shari'a, amma ta soke umarnin da ya sa INEC ta cire sunayen shugabannin ADC na tsagin Mark.
Atiku ya yi maraba da hukuncin
Manyan jiga-jigan ADC sun fara nuna murna kan wannan nasara, inda aka ji tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi maraba da wannan hukunci.
Da yake mayar da martani jim kaɗan bayan kotun koli ta amince da Mark a matsayin shugaban jam'iyyar, Atiku ya gargaɗi magoya bayan, yana mai gargaɗin cewa akwai ƙarin aiki a gaba a ƙoƙarin "ceto" ƙasar.

Source: Facebook
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, dan takarar shugaban kasar ya bayyana hukuncin a matsayin wani ci gaba, amma ya jaddada cewa bai kamata a yi kuskuren daukarsa a matsayin nasara ta karshe ba.
Kotu ta hana INEC aminta da taron ADC
An ji cewa wata babbar kotun tarayya ta soke babban taron jam'iyyar ADC na kasa, kuma ta hana hukumar zaben Najeriya (INEC) amincewa da shi.
Ta kuma hana tsohon Sshugaban majalisar dattawa, David Mark, da wasu jiga-jigan ADC tsoma baki cikin ayyuka da wa’adin shugabannin jam'iyya jihohi.
Wadanda suka shigar da kara sun ce shugabancin rikon kwarya da aka nada karkashin jagorancin Sanata David Mark, ba shi da hurumin gudanar da tarukan jihohi ko kafa kwamitin da zai yi hakan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

