INEC: Najeriya na Iya Kafa Tarihi kan Yawan Masu Kada Kuri' a Babban Zaben 2027

INEC: Najeriya na Iya Kafa Tarihi kan Yawan Masu Kada Kuri' a Babban Zaben 2027

  • Hukumar INEC ta ce adadin wadanda suka yi rajistar zaɓe a Najeriya zai haura miliyan 100 gabanin babban zaɓen 2027
  • Hakan zai sanya Najeriya ta zama ƙasar da ke da mafi yawan masu zaɓe a fadin kasashen nahiyar Afirka
  • Hukumar ta buƙaci jami’anta su ƙara wayar da kan masu zaɓe tare da yaƙi da yaɗa bayanan ƙarya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta yi hasashen cewa adadin mutanen da aka yi wa rajistar zaɓe a Najeriya zai haura miliyan 100 gabanin babban zaɓen 2027.

Kwamishinan INEC na Ƙasa kuma shugaban Kwamitin Yaɗa Bayanai da Ilimantar da Masu Zaɓe (IVEC), Mohammed Haruna, ne ya bayyana hakan ranar Talata, 18 ga watan Agusta, 2026 a Abuja.

INEC.
Shugaban hukumar zabe ta kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan yana jagorantar taro da kwamishinonin zabe Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Premium Times ta ruwaito cewa Haruna ya yi magana ne a taron haɗin gwiwa na sassan Ilimantar da Masu Zaɓe da Yaɗa Bayanai (VEP) domin shirye-shiryen babban zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Dama ga matasa: Hukumar INEC za ta ɗaauki ma'aikata miliyan 1.4 a zaben 2027

Masu zaɓe za su haura miliyan 100

An gudanar da taron ne domin tsara taswirar sadarwa da haɗa kowa cikin babban zaɓen 2027, domin tabbatar da gudanar da zaɓe cikin ’yanci, adalci, sahihanci, da zaman lafiya

Haruna ya ce kundin rajistar masu zaɓe na baya yana da sama da mutane miliyan 93, kuma ana sa ran adadin zai haura miliyan 100 bayan kammala tantance sakamakon rajistar masu zaɓe da aka gudanar a faɗin ƙasar.

A cewarsa, hakan zai sanya Najeriya ta zama ƙasar da ke da mafi yawan masu zaɓe a tsarin dimokuraɗiyya a kaf nahiyar Afirka.

INEC ta nemi karin wayar da kai

Kwamishina ya ce saura kwanaki 151 kafin fara zagayen farko na babban zaɓen, don haka jami’an yaɗa bayanai na INEC su tabbatar da isar da saƙonni masu inganci domin jawo dukkan ’yan ƙasar da suka cancanci kaɗa ƙuri’a.

Zabe.
Ma'aikatan INEC yayin da suke aikin tantance masu iafa kuri'a a zaben gwamnan jihar Anambra Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

Ya ce aikin na da sauƙi a wasu ɓangarori amma kuma yana da wahala saboda yawan masu zaɓen da za a yi wa bayanin, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

INEC ta yi maganar goyon bayan wani dan takara ko jam'iyya a zaben 2027

“Dole ne aikinmu ya kasance na samar da mafi faɗi da inganci wajen yaɗa bayanai game da dukkan nau’o’in zaɓe biyar domin jawo ’yan Najeriya da suka kai shekarun kaɗa ƙuri’a su zaɓi shugabanninsu,” in ji shi.

INEC za ta maye gurbin dan Majalisa

A wani labarin, kun ji cewa hukumar INEC ta sanya Asabar, 19 ga Satumba, 2026, domin gudanar da zaɓen cike gurbin dan Majalisar mazabar Gombe/Kwami/Funakaye.

Za a gudanar da zaɓen ne bayan rasuwar ɗan majalisar wakilai mai wakiltar wannan mazaba ta jihar Glmbe, Yaya Bauchi Tongo.

Hukumar INEC ta ce za a gudanar da zaɓen bisa Sashe na 76(2) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, wanda aka yi wa kwaskwarima, da kuma tanade-tanaden Dokar Zaɓe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262