Matakin da INEC Ta Dauka kan Shugabancin ADC bayan Hukuncin Kotun Koli

Matakin da INEC Ta Dauka kan Shugabancin ADC bayan Hukuncin Kotun Koli

  • Kotun Koli ta yanke hukunci kan shari'ar da ake yi dangane da rigimar shugabancin jam'iyyyar ADC mai adawa
  • Hukuncin da Kotun Kolin ta yanke ya soke wanda kotun daukaka ta zartar wanda ya sa hukumar INEC daina amincewa da shugabancin ADC karkashin David Mark
  • Biyo bayan hukuncin na Kotun Koli, INEC ta sauya matsayar da ta dauka kan shuganancin ADC mai adawa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sabunta shafinta na yanar gizo, biyo bayan hukuncin Kotun Koli kan shugabancin jam'iyyar ADC.

Hukumar INEC ta lissafa David Mark a matsayin shugaban jam’iyyar ADC na kasa da Rauf Aregbesola a matsayin sakatarenta ƙasa, biyo bayan hukuncin Kotun Koli.

INEC ta amince da shugabancin ADC
Shugaban hukumar zabe ta INEC, Farfesa Joash Amupitan da tambarin jam'iyyar ADC Hoto: @inecnigeria
Source: Twitter

An lura da hakan ne a shafin yanar gizo na INEC da yammacin ranar Alhamis, 30 ga watan Afrilun 2026.

Kara karanta wannan

Rikicin ADC: Da gaske an kona gidan Nafiu Bala a Gombe? an samu gaskiya

INEC ta amince da su David Mark

Wannan ci gaba ya soke matakin da INEC ta ɗauka a farkon watan Afrilu na cire shugabancin da Mark ke jagoranta daga shafinta, inda ta dogara da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara kan rikicin shugabancin ADC.

Bangarorin ADC ƙarƙashin David Mark da kuma Nafiu Bala, tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa, sun dade suna takaddama kan shugabancin jam’iyyar.

Kotun Koli ta yi hukunci kan shugabancin ADC

Jaridar TheCable ta ce a ranar Alhamis, Kotun Koli ta umarci David Mark da ya koma babbar kotun tarayya domin sauraro da kuma yanke shawara kan al’amuran da suka taso daga takaddamar shugabancin a cikin ADC.

Yayin da yake yanke hukuncin bai-ɗaya, kwamitin alƙalai biyar na Kotun Kolin, ƙarƙashin jagorancin Mohammed Garba, ya soki umarnin kotun ɗaukaka ƙara wanda ya buƙaci ɓangarorin da su ci gaba da kasancewa yadda suke kafin fara rikicin.

An ga sunayen shugabannin ADC a INEC

Biyo bayan wannan hukunci, wurin ADC a shafin yanar gizo na INEC, wanda aka cire a baya, yanzu ya nuna cikakken jerin shugabannin jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Mark.

Kara karanta wannan

Wike ya yi magana bayan hukuncin Kotun Koli kan rikicin shugabancin PDP, ADC

Ya zuwa ƙarfe 11:00 na daren ranar Alhamis, shafin yanar gizo na INEC ya nuna Mark ne ke jagorantar ADC.

INEC ta amince da shugabancin ADC karkashin David Mark
Shugaban jam'iyyar ADC na kasa, David Mark na gaisawa da Atiku Abubakar Hoto: @Atiku
Source: Twitter

Hakazalika shafin ya nuna Rauf Aregbesola a matsayin sakataren jam'iyya na ƙasa, Dr. Mani Ahmad a matsayin ma'ajin jam'iyya ƙasa, Akibu Dalhatu a matsayin sakataren kuɗi na ƙasa, da kuma Farfesa Oserheimen Osunbor a matsayin mai ba jam’iyya shawara kan shari’a na ƙasa.

Hukuncin Kotun Kolin ya soke umarnin kotun daukaka kara wanda a baya ya dakatar da batun shugabancin, kuma ya umarci da a mayar da dukkan shari’un da suka shafi hakan zuwa Babbar Kotun Tarayya.

INEC za ta gudanar da zabe

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta shirya gudanar da zabubbukan cike gurbi a wasu jihohi.

Hukumar zaben ta INEC za ta gudanar da zaben cike gurbin ne a jihar Kano da wasu jihohi biyar a cikin watan Yunin 2026.

Zaɓubbukan za su haɗa da kujerun sanatoci a jihohin Enugu, Nasarawa, Rivers da Ondo, da kuma kujera ta majalisar dokokin jihar Kebbi da kujera ta majalisar wakilai a jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng