Bayan an Yi Masa Tayin Takara, Shugabannin NDC Sun Gana da Kwankwaso a Gidansa

Bayan an Yi Masa Tayin Takara, Shugabannin NDC Sun Gana da Kwankwaso a Gidansa

  • Tsohon ɗan takarar Shugaban ƙasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya karɓi shugabannin NDC a Abuja
  • Ana zargin sun nemi ya shiga jam’iyyarsu gabanin zaɓen 2027 yayin da rikicin shugabanci ke ci gaba da ba ADC wahala
  • Wannan sabon tayi na zuwa ne bayan sun nemi Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da Peter Obi su tsaya masu takara a 2027

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya karɓi bakuncin wasu manyan shugabannin jam’iyyar NDC a ranar Litinin 27 ga watan Afrilu, 2026 a Abuja.

Rahotanni sun nuna cewa ganawar ta gudana ne a gidansa da ke babban birnin tarayya, inda aka tattauna batutuwan siyasa da suka shafi makomar zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya samu wanda za su fafata wajen neman tikitin APC a zaben 2027

NDC ta kai wa Kwankwaso ziyara
Sanata Rabi'u Musa kwankwaso, a gefe kuma yana tare da manyan NDC da suka ziyarce shi Hoto: Rabi'u Musa Kwankwaso/Nigeria Democratic Congress Kano chapter
Source: Facebook

Jaridar The Cable ta wallafa cewa daga cikin waɗanda suka halarci ganawar akwai Mohammed Bakin, mataimakin shugaban NDC na ƙasa na shiyyar Arewa maso Yamma.

Abin da Kwankwaso ya gana da NDC

Duk da babu wata sanarwa a hukumance daga bangarorin biyu game da cikakken abin da suka tattauna, amma majiyoyi sun bayyana cewa haɗin gwiwa na daga cikin batutuwan da suka taso.

Wasu majiyoyi daga cikin tafiyar Kwankwasiyya sun shaida cewa shugabannin NDC sun roƙi Kwankwaso da ya shiga jam’iyyarsu domin haɗa ƙarfi kafin babban zaɓen 2027.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta yayatawa cewa Kwankwaso na duba yiwuwar sauya sheƙa ko kuma yin haɗin gwiwa da wasu ‘yan siyasa domin tunkarar zaɓe mai zuwa.

Kwankwaso ya shiga haɗakar siyasa

Tun farkon wannan wata, ana ta rade-radin cewa Kwankwaso, wanda jagora ne ne a ADC, na nazarin yiwuwar yin takara tare da Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

Kwankwaso, Peter Obi sun samu tayin tikitin takara kai tsaye a zaɓen 2027

NDC na son Kwankwaso ya sauya sheka
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa Rabi'u Musa Kwankwaso Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Duk da cewa babu tabbaci kai tsaye daga bakin Kwankwaso da kansa, amma wannan jita-jita na kara ƙara zafi a harkar siyasar ƙasar.

A makon da ya gabata, magoya bayan Obi da Kwankwaso sun ƙaddamar da wata tafiya mai suna “OK Movement”, wacce ke da nufin tara goyon baya ga shugabannin biyu.

Wannan mataki ya kara nuna yiwuwar haɗakar ‘yan adawa domin kalubalantar jam’iyyun da ke kan mulki.

Sai dai a lokaci guda, jam’iyyar ADC na fuskantar rikicin shugabanci da ke barazana ga tsayuwarta a zaɓen 2027.

Kwankwaso da Obi sun samu tayin takara

A baya, mun wallafa cewa jam’iyyar NDC ta tura roko na musamman ga tsohon yan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso.

NDC ta roke su da su sauya sheka daga ADC zuwa gare ta domin fafatawa zaɓen 2027, tare da ba su damar tikitin shugaban ƙasa a babban zaben da ke tafe.

Rikicin shugabanci da ke addabar ADC da kuma jadawalin INEC na gabatar da sunayen ‘yan takara ya ƙara jefa jam’iyyun adawa cikin matsin lamba kan 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng