Kotun Koli: Abin da Zai Sa Jam'iyyar ADC Ta Rasa Damar Shiga Zaben 2027 a Najeriya

Kotun Koli: Abin da Zai Sa Jam'iyyar ADC Ta Rasa Damar Shiga Zaben 2027 a Najeriya

  • Rikicin shugabanci da ke addabar jam'iyyar ADC na iya hana ta shiga babban zaben 2027 idan har Kotun Koli ta yi jinkirin yanke hukunci
  • Kotun Kolin Najeriya ta bayyana cewa za ta sanya ranar da za ta dawo domin yanke hukunci kan rikicin shigabanci na jam'iyyun ADC da PDP
  • Bisa ga tanadin jadawalin zaben 2027, ADC na iya rasa damar tsaida yan takara idan Babban kotun kasar ba ta yi hukunci nan da kwanaki 18 ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - A jiya Laraba, 22 ga watan Afrilu, 2026, Kotun Kolin Najeriya ta yi zaman sauraron korafe-korafen da suka shafi manyan jam'iyyun adawa, ADC da PDP.

A zaman Kotun Koli ta ce za ta yanke hukunci nan gaba kan ƙorafe-ƙorafen da suka shafi rikicin shugabanci a jam’iyyun PDP da ADC, bayan sauraron dukkan ɓangarorin da ke da ruwa da tsaki.

Kara karanta wannan

Atiku da Kwankwaso na tsaka mai wuya, Kotun Koli ta zo matakin karshe kan rikicin ADC

Shugaban ADC.
Shugaban tsagin ADC na kasa, David Mark tare da jagoran adawa, Atiku Abubakar a taron manema labarai a Abuja Hoto: @Atiku
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa kotun ba ta bayyana ranar da za ta yanke hukuncin ba, lamarin da ya haifar da rashin tabbas ga ɓangarorin da ke rikici a cikin jam’iyyun biyu.

Halin da jam'iyyar PDP ke ciki

A bangaren PDP, rikicin ya riga ya sauya tsarin shugabancin jam’iyyar, bayan hukuncin kotuna sun soke taron Ibadan da ya haifar da zaɓen Kabiru Turaki a matsayin shugaban PDP na kasa

Wannan na nufin cewa shugabancin PDP da Hukumar Zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta amince da shi, wanda ke da goyon bayan Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, shi ne zai ci gaba da jagoranci har sai Kotun Koli ta yanke hukunci.

Bangaren Wike ya samu nasara har a kotun daukaka kara don haka aka yi waje da Tanimu Turaki.

ADC na cikin gagarumar matsala

Sai dai a bangaren ADC, al’amura sun fi rikitarwa, domin babu wani bangare daga cikin ɓangarori uku da ke iƙirarin shugabancin jam'iyya da INEC ta amince da shi.

Kara karanta wannan

Bayan sauya shekar Kwankwaso, wasu manyan jiga jigan siyasar Najeriya za su koma ADC

Waɗannan ɓangarorin sun haɗa da na Sanata David Mark, Nafiu Bala Gombe da Ogga Temitope, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

ADC .
Tambarin jam'iyyar hadakar yan adawar Najeriya, ADC Hoto: ADC Party
Source: Twitter

ADC na iya rasa damar shiga zabe

Dukkan jam’iyyun siyasa da aka yi rajista dole ne su gabatar da jerin sunayen mambobinsu ga INEC kafin ranar 10 ga Mayu, domin samun damar tsayar da ‘yan takara a zaɓen 2027.

Saboda haka, idan Kotun Koli ba ta yanke hukunci cikin kwanaki 18 masu zuwa ba, akwai yiwuwar jam’iyyar ADC ba za ta samu damar shiga zaɓen 2027 ba.

'Yan ADC za su hade da jam'iyyar PRP?

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta musanta rahotannin da ake yadawa cewa ta fara tattaunawa da PRP domin kulla kawance kafin babban zaben 2027 mai zuwa.

An yi ta samun rade-radin cewa shugabannin adawa na iya neman haɗewa da wasu jam’iyyun siyasa, ciki har da PRP domin kalubalantar gwamnatin APC.

ADC ta bayyana iƙirarin a matsayin ƙarya, inda ya nuna cewa shugabancin haɗakar jam’iyyun ba su cikin wata tattaunawa da wata jam’iyyar siyasa a halin yanzu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262