'Yan Sanda Sun Yi Ruwan Wuta kan 'Yan Bindiga a Sokoto, an Kashe Miyagu
- Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sokoto ta hallaka wasu da ake zargi ’yan bindiga ne tare da kama wasu mutane 11
- Ta kwato bindigogin AK-47 guda biyu, harsasai 54, jigidar bindiga da kuma babura 14 da aka sace a ayyukan da aka gudanar tsakanin 14 da 15 ga Agusta, 2026
- ’Yan sanda sun dakile wani yunkurin harin ’yan bindiga a Dankadu da ke Karamar Hukumar Illela, inda aka kashe biyu daga cikin wadanda suka tsere da raunukan harbin bindiga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Sokoto - Rundunar ’yan sandan Jihar Sokoto ta hallaka wasu da ake zargi ’yan bindiga biyu tare da kama wasu 11 a wasu ayyuka da ta gudanar kan ’yan bindiga, satar babura da sauran laifuffuka a fadin jihar.
Rundunar ta kuma kwato bindigogin AK-47 guda biyu, harsasai 54, jigida biyu, bindigar hannu da aka kera a gida da kuma babura 14 da aka sace a ayyukan da aka gudanar tsakanin 14 da 15 ga Agusta, 2026.

Source: Original
Ahmad Rufa’i, jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, 19 ga watan Agustan 2026, cewar rahoton jaridar The Punch.
A cewar sanarwar, ayyukan sun hada da dakile wani yunkurin harin ’yan bindiga a kauyen Dankadu da ke Karamar Hukumar Illela.
An dakile harin Dankadu
Rundunar ta ce ta samu kiran neman agaji da misalin karfe 9:00 na dare ranar 15 ga Agusta, inda aka sanar da ita cewa wasu ’yan bindiga dauke da makamai suna dosowa daga Dajin Tsauana zuwa kauyen Dankadu.
Nan take aka tura jami’an Sashin Yaki da Satar Mutane, Volunteer Constabulary da Rescue Unit, tare da wasu rundunonin musamman zuwa yankin.
Sanarwar ta ce jami’an sun yi arangama mai tsanani da ’yan bindigar, inda aka yi musayar wuta na tsawon lokaci.
Rundunar ta ce ’yan bindigar sun kasa jure karfin makaman jami’an tsaro, lamarin da ya sa suka tsere zuwa cikin daji dauke da raunukan harbin bindiga.
'Yan sanda sun kashe 'yan bindiga
Daga bisani, binciken da jami’an suka gudanar a yankin ya kai ga hallaka biyu daga cikin ’yan bindigar da suka tsere tare da kwato bindigogin AK-47 guda biyu, jigida biyu da harsasai 54.
Rundunar ta ce babu wani jami’in tsaro ko mazaunin yankin da aka kashe yayin samamen.
Ta kara da cewa ana ci gaba da gudanar da sintiri a yankin domin karfafa gwiwar mazauna tare da tabbatar musu da cewa suna cikin aminci.
An kama masu satar babura
A wani samame na daban da aka gudanar kan wata kungiyar masu satar babura da ke aiki a yankunan Kwannawa da Tamaje na cikin birnin Sokoto, an kama wasu mutane uku.
Rundunar ta bayyana wadanda aka kama da sunayen Siba Abdullahi na kauyen Dimbiso da ke Karamar Hukumar Wurno; Hassan Hassan na Tamaje; da Usama Isah na Unguwar Rogo.
Rundunar ta kuma ce rundunar Strike Force ta kama wasu mutane da ake zargi da kasancewa cikin wata babbar kungiyar da ke da hannu wajen satar babura, karbar kudin fansa, jabun takardu da karbar kayan sata.
Ta ce samamen ya biyo bayan korafe-korafen da shugabannin al’umma a Mana Babba, Mabera, Unguwar Rogo da Tamaje suka gabatar kan karuwar satar babura da sauran ayyukan laifi.

Source: Twitter
'Yan bindiga sun kashe mutane
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga ne sun kashe mutane sama da 20 a ƙauyen Binper da ke gundumar Bwai a ƙaramar hukumar Mangu ta Jihar Plateau.
shugaban ƙungiyar Raya Al’ummar Mwaghavul (MDA), Bulus Dabit, ya ce maharan sun mamaye ƙauyen ne da tsakar dare, a lokacin da mutane ke barci.
Asali: Legit.ng


