2027: Shettima Ya Yi Gargadi kan Rusa APC bayan Zaben Fitar da Gwani

2027: Shettima Ya Yi Gargadi kan Rusa APC bayan Zaben Fitar da Gwani

  • Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya yi magana game da zaben fitar da gwani da jam'iyyar APC za ta gudanar a jihohi
  • Ya yi kira ga dukkan masu shirin shiga takara da su kasance tare da jam'iyyar APC ko da ba su yi nasara ba a zaben fitar da gwani
  • A yanzu haka dai masu sha'awar shiga takara a matakai daban-daban a zaben sun fara sayen fom da jam'iyyar APC mai mulki ke sayarwa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Mataimakin Shugaban kasa, Kashim Shettima, ya gargadi masu neman tikitin jam’iyyar APC gabanin zaben 2027 da kada su rusa jam’iyyar idan wasu sun kayar da su a zaben fitar da gwani.

A cikin wata makala da ya rubuta, ya bayyana cewa duk da bambancin manufofi, magoya baya, yankuna da ra’ayoyi, dole ne su tuna cewa duk suna cikin gida guda na siyasa.

Kara karanta wannan

Ana jiran hukuncin kotu: David Mark ya fadi abin da zai faru da ADC a zaben 2027

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima
Kashim Shettima na zaune a ofis a Abuja. Hoto: Kashim Shettima
Source: Twitter

Kiran Shettima ga 'yan APC

Legit Hausa ta tattaro bayanan da Kashim Shettima ya yi ne a wani sako da hadiminsa, Stanley Nkwocha ya wallafa a shafinsa na X.

Shettima ya yi kira da cewa:

“Dole ne mu guji fadawa tarkon 'yan jarida, masu neman tayar da fitina, masu anfani da rikici, ko wadanda ke cin moriya daga rabuwar kai. A ko da yaushe za a samu masu yada jita-jita cewa an tauye wani shugaba, ko an ware wani bangare.

“Wadannan dabaru ne da ake amfani da su a siyasa domin jefa shakku da rusa hadin kai kafin ma a fara takara.

Magana kan 'yan takarar APC

Rahoton NAN ya nuna cewa Shettima ya kara da cewa darasi mafi muhimmanci a siyasa shi ne cewa a karshe mutum daya ne kawai zai samu tikiti.

“Mutane da yawa za su nemi takara, za su kashe kudi, za su yi fatan samun nasara, za su samu goyon bayan magoya baya.

Kara karanta wannan

Bayan an yi masa tayin takara, shugabannin NDC sun gana da Kwankwaso a gidansa

"Amma a karshe suna daya ne za a zaba. Wannan ba rashin adalci ba ne, sakamakon tsarin dimokuradiyya ne.”

Shettima ya yi magana kan juriya da hakuri, inda ya ce:

“Kowa na iya murna idan ya yi nasara, amma hakuri da jure rashin nasara ne ke nuna halin mutum.”

Kiran Shettima ga shugabannin APC

Mataimakin shugaban kasar ya kuma bukaci shugabannin jam’iyya da su yi adalci tare da girmama dukkan masu neman takara.

Ya ce:

“Dole ne wakilai su yi zabe ba tare da tsoro ba. Dole ne tsarin ya kasance a bude yadda kowa zai girmama shi, har da wadanda suka fadi.
"Idan akwai korafe-korafe, a saurare su da adalci. Idan akwai jita-jita, a fayyace su.”

Ya kuma roki wadanda za su iya faduwa a zaben fitar da gwani da su yi hakuri.

“Siyasa tafiya ce mai tsawo. Ba a kona abin hawa saboda tangarda daya, kuma ba a daina tafiya saboda wata kofa ta rufe.
“Tarihi ya nuna mutane da dama sun fadi yau suka yi nasara gobe. Wasu an yi watsi da su a wani lokaci amma daga baya suka zama masu muhimmanci.”

Kara karanta wannan

2027: An kunna rikici a PRP da ke shirin kawar da Tinubu, ADC ta magantu

Kashim Shettima da Bola Tinubu
Kashim Shettima na gaiswa da Bola Tinubu a fadar shugaban kasa. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

An zabi dan takarar APC a Yobe

A wani labarin, mun kawo muku cewa masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a jihar Yobe sun zabi wanda zai masu takara a zaben 2027.

Jagororin APC sun zabi tsohon sakataren gwamnatin Yobe, Baba Malam Wali a matsayin wanda suka amince da shi ya gaji Mai Mala Buni.

Gwamna Mai Mala Buni ya kasance a wajen da shugabannin APC suka taru a Abuja domin amincewa da Baba Malam Wali a matsayin dan takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng