Jarumar Fim Ta Fito Takarar Gwamna, Ta Aika Sakon da Zai Girgiza Gwamna Mai Ci

Jarumar Fim Ta Fito Takarar Gwamna, Ta Aika Sakon da Zai Girgiza Gwamna Mai Ci

  • Jaruma Doris Ogala ta bayyana aniyarta ta neman kujerar gwamnan jihar Abia a zaben 2027 da ake tunkara
  • Doria Ogala ta ce shawarar tsayawa takara ta samo asali ne daga “kiran Ubangiji” da ta ce ya ba ta umarnin ceto al’ummar Abia
  • Jarumar ta soki gwamnatin Alex Otti, tana mai cewa ba a samar da wutar lantarki ta sa’o’i 24 a jihar ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Abia - Jarumar fina-finai ta masana'antar Nollywood, Doris Ogala ta bayyana aniyarta ta zama gwamnar jihar Abia.

Jaruma Doris Ogala ta bayyana kudirinta na tsayawa takara a matsayin “umarnin Ubangiji”.

Doris Ogala ta fito takarar gwamnan Abia
Jaruma Doris Ogala da Gwamna Alex Otti na jihar Abia Hoto: Doris Ogala U, Alex C Otti
Source: Facebook

Ogala ta bayyana hakan ne yayin wani shiri na Clarity Zone podcast, inda ta nuna kwarin gwiwar cewa za ta zama gwamnar jihar Abia ta gaba, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

An zo wajen: Trump ya fadi babban burin gwamnatinsa kan Iran

A cewarta, shawarar neman kujerar gwamnan jihar ta samo asali ne daga abin da ta kira kiran Ubangiji na ceton al’ummar Abia.

“Kiran da aka yi mini na zo na ceci jama’ata umarnin Ubangiji ne. Ni ce zan zama gwamnar jihar Abia ta gaba, kuma babu abin da zai hana hakan.”

Ogala ta yarda da kanta

Da aka tambaye ta dalilin da ya sa take da cikakken yakinin cewa za ta zama gwamna, Ogala ta ce ta yi imanin cewa ta fi sauran masu neman kujerar cancanta.

“Na tabbatar da hakan sosai, kuma na san haka ne saboda na fi dukkansu cancanta.”

Ogala ta kuma soki gwamnatin Gwamna Alex Otti, tana mai zargin cewa gwamnati ba ta yi abin da ya kamata ba wajen inganta yanayin rayuwar jama’a a jihar.

Musamman ta kalubalanci ikirarin da ake yi kan samun wutar lantarki a Abia, inda ta ce mazauna jihar ba sa samun wutar lantarki na tsawon sa’o’i 24 duk da irin ikirarin da ake yi.

Kara karanta wannan

Matar aure ta sace jariri bayan kwashe watanni tana zabgawa mijinta karya

Ta ce babu wutar lantarki ta sa’o’i 24 a Abia, tana mai cewa abin da ake nunawa a kafafen sada zumunta bai yi daidai da halin da ake ciki a zahiri ba.

Ta yi magana kan kasuwar Ariaria

Ogala ta kuma musanta ikirarin da ake yi kan ci gaban kasuwar Ariaria International Market da ke Aba.

Ta dage cewa bangaren A-Line na kasuwar ne aka gina a lokacin gwamnatin tsohon gwamna Okezie Ikpeazu.

"Ina kalubalantar gwamnan ya musanta ni. Bai gina Ariaria ba. Wurin da aka gina a Ariaria shi ne A-Line, kuma Ikpeazu ne ya gina shi. John Okiyi ne kwamishina a lokacin.”

Doris Ogala, wadda ta ce tana cikin gwamnatin Ikpeazu, ta jaddada cewa tana magana ne bisa abin da ta sani da kanta game da aikin.

Doris Ogala ta yi magana kan zaben 2027
Jarumar fim, Doris Ogala Hoto: Doris Ogala U
Source: Facebook

Peter Obi ya ba 'yan siyasa shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya bukaci masu ruwa da tsaki a siyasa su tabbatar da cewa babu dan Najeriya da ya rasa ransa saboda zabe.

Peter Obi ya kuma yi kira ga ’yan takara su gudanar da kamfen bisa batutuwa gabanin babban zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng