Obasanjo Ya Shiga Gaba, zai Jagoranci 'Yan Adawa Karfafa Yaki da APC, Tinubu
- A yau Asabar, 25 ga watan Afrilun 2026 gamayyar jam'iyyun adawa za su gudanar da wani muhimmin taro a jihar Oyo game da 2027
- Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ne zai jagoranci taron domin karfafa 'yan adawa da farfado da tsarin dimokuradiyya.
- Jam'iyyar PDP ta sannar da cewa za a gudanar da taron ne a gidan gwamnatin jihar Oyo da ke Ibadan karkashin gwamna Seyi Makinde
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Oyo - Shugabannin manyan jam'iyyun adawa a Najeriya za su gudanar da taro na musamman a Oyo game da siyasar shekarar 2027.
Jam'iyyar adawa ta ADC da ta hada Atiku Abubakar, Rabiu Kwankwaso, Nasir El-Rufa'i, Peter Obi, Rotimi Ameachi za ta halarci wajen taron.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanai game da yadda taron 'yan adawan zai gudana ne a wani sako da jam'iyyar PDP ta wallafa a shafinta na X..
Bayani kan taro 'yan adawa a Oyo
A sanarwar da PDP ta fitar, ta bayyana cewa taron da 'yan adawa za su yi a Ibadan zai iya kawo sauyi a yanayin siyasar Najeriya a yau.
Ta ce:
"A wani babban taro mai muhimmanci da ake ganin zai iya sauya alkiblar siyasar ƙasar nan, shugabannin manyan jam’iyyun adawa sun shirya taruwa a yau a babban dakin taro na fadar gwamnati da ke Ibadan domin gudanar da taron kasa na shugabannin jam’iyyun adawa."
Rahoto ya nuna cewa an tsara taron ne karkashin take mai cewa “mu hada kai domin gina tafiyar adawa mai karfi mu kare dimokuradiyyarmu.”
PDP ta bayyana cewa ana sa ran taron zai zama wata hanya ta tsara dabaru domin tinkarar kalubalen tattalin arziki da tsaro da suke addabar Najeriya a halin yanzu.
Obasanjo zai jagoranci taron
Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo, ne zai jagoranci taron a matsayin shugaba, yayin da Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, zai kasance mai masaukin baki.
Ana ganin Obasanjo a matsayin jigo a Najeriya kasancewar ya mulki kasar a lokuta daban-daban da suka hada da karshin mulkin soja da tsarin dimokuradiyya.
Sauran shugabannin da za su hallara taron domin bayani sun hada da tsohon dan majalisar wakilai daga jihar Katsina, Dr Usman Bugaje.

Source: Facebook
Farfesa Pat Utomi, Dr Kabiru Adamu, Barista Mike Igini da lauya mai kare hakkin dan Adam, Farfesa Chidi Odinkalu za su hallara wajen taron.
Hadimin Sanata Rabiu Kwankwaso, Saifullahi Hassan ya wallafa hotunan wasu 'yan Kwankwasiyya da suka riga suka isa jihar Oyo a shafinsa na Facebook.
'Ana son rusa taron mu,' ADC
A wani labarin, mun kawo muku cewa jam'iyyar adawa ta ADC ta yi zargin cewa APC na son kawo mata cikas game da taron da za ta yi a Ibadan.
Kakakin ADC na kasa, Bolaji Abdullahi ya yi zargin cewa APC na musu haka ne bayan yunkurin hana su taro a Abuja bai yi nasara ba.
A sanarwar da ya fitar, Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa babu gudu babu ja da baya kan taron da za su yi duk da abubuwan da suke ji ta bayan fage.
Asali: Legit.ng

