2027: An Kunna Rikici a PRP da Ke Shirin Kawar da Tinubu, ADC Ta Magantu
- Wani sabon rikici ya bulla jam'iyyar adawa ta PRP bayan rade-radin cewa masu hadaka a ADC za su koma can domin tunkarar Bola Tinubu
- Shugaban jam'iyyar PRP, Hakeem Baba-Ahmed ya yi magana kan rikicin, inda ya nuna cewa shi ne sahihin jagoran PRP a Najeriya
- Jam'iyyar ADC ta zargi APC da kunna wutar rikici a PRP, duk da cewa jam'iyya mai mulki na nesanta kanta da rikicin 'yan adawa kasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaban jam’iyyar PRP na kasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya yi Allah-wadai da yunkurin da wasu ke yi na kirkirar bangarori a cikin jam’iyyar.
Hakeem Baba-Ahmed ya mayar da martani ne ga wata kungiya mai suna PRP-Vanguard Collective, da ta ki amincewa da sakamakon babban taron jam’iyyar na kasa da ya samar da shugabancin da ake da shi a yanzu.

Source: UGC
Daily Trust ta wallafa cewa shugaban kungiyar, Kwamared Abdulmajid Yakubu Daudu ya bayyana taron PRP a matsayin “na bogi”, tare da zargin wata kungiyar daban da kokarin kwace jam’iyyar.
Martanin shugaban RPR na kasa
Da yake mayar da martani kan sabon rikicin da ke shirin bulla, Dr Hakeem Baba-Ahmed ya ce babu wani aibi a taron da ya samar da shugabancinsa.
“Ba a samu wata matsala ba ko kadan. Mun yi sa’a domin dukkan matakan da doka ta tanada wajen tabbatar da sahihancin shugabancin nan sun cika.
"Mun san akwai wata manufa a bayan wannan, amma muna ganin masu yin hakan suna da niyya mai kyau, kuma muna son mu zauna da su mu tattauna,”
In ji shi.
Hakeem Baba-Ahmed dan PRP ne
Game da zargin cewa shi ba dan jam’iyyar PRP ba ne, Baba-Ahmed ya ce ya shiga jam’iyyar fiye da shekaru 10 da suka gabata, kuma shi ne ya jagoranci zaben fidda gwani da ya samar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a Kano a baya.
Dangane da ko akwai rikici a cikin jam’iyyar, shugaban ya tunatar da cewa an taba samun shari’a tsakanin PRP da tsohon shugabanta tare da wasu mutum 12, inda aka yanke hukunci a ranar 31 ga Agusta, 2022.
Martanin ADC kan rikicin PRP
Jim kadan bayan bayyanar rudani a PRP, kakakin jam'iyyar ADC, Bolaji Abdullahi ya fitar da sanarwa a X yana zargin APC da kunna wutar rikicin.
Ya ce:
"Kimanin mako uku da suka gabata, shugabannin PRP karkashin jagorancin Baba-Ahmed sun kai ziyara ga shugaban jam’iyyar ADC na kasa.
"Bayan ‘yan kwanaki, sai jita-jita suka fara yawo cewa ana tunanin 'yan ADC za su koma PRP. Ko da yake hakan ba gaskiya ba ne, amma wannan jita-jitar kadai ta sa aka fara ganin wani sabon bangare a jam'iyyar.
"Ana kallon wannan a matsayin wani bangare hana 'yan adawa sakat a Najeriya karkashin jam’iyyar APC.

Source: Facebook
Ya kara da cewa:
"Duk da cewa gwamnati na musanta hannu a rikice-rikicen da ke faruwa a jam’iyyun adawa, tana mai cewa matsalolin cikin gida ne kawai, amma alamu sun nuna wani salo da ke bayyane ga kowa."
'Yan adawa sun yi taro a Ibadan
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyun adawa sun gudanar da wani taron hadin kai a gidan gwamnatin Oyo da ke Ibadan game da zaben 2027.
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ne ya jagoranci zaman, yayin da gwamna Seyi Makinde ya kasance mai masaukin baki.
Rahotanni sun nuna cewa Atiku Abubakar, Rabiu Musa Kwankwaso, Peter Obi, Rotimi Ameachi da sauran manyan 'yan adawa sun hallara taron.
Asali: Legit.ng


