Abin a Yaba da Tinubu Ya Yi Ana Daf da Sake Sakamakon Zaben Osun, Ya Sha Yabo
- Jigo a jam’iyyar Accord, Pelumi Olajengbesi, ya yi magana game da abin kirki da Shugaba Bola Tinubu ya yi masu kafin sanar da sakamako
- Olajengbesi ya yaba wa Tinubu saboda rashin tsoma baki cikin zaben, amma ya ce ba za a bayyana zaben a matsayin cikakken ‘yanci ba
- Ya ce an kama wasu magoya bayan adawa yayin zaben, yayin da Adeleke ya samu kuri’u 511,067, ya doke Bola Oyebamiji na APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Osogbo, Osun - Majiyoyi sun tabbatar da cewa Shugaba Bola Tinubu ya taya Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, murnar samun nasara a zaben gwamna.
Wani wani jigon jam’iyyar Accord da ta yi nasara a zaben da aka gudanar a jiya Asabar, Pelumi Olajengbesi ne ya tabbatar da rahoton.

Source: Twitter
Olajengbesi ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da manema labarai a cibiyar tattara sakamakon zaben hukumar INEC da ke Osogbo, jim kadan bayan sanar da Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben, cewar Vanguard.
Abin da Tinubu ya yi a zaben Osun
Ya yaba wa Shugaba Tinubu saboda abin da ya bayyana a matsayin shawarar shugaban na kin tsoma baki cikin harkar zaben.
A cewarsa, hakan ya nuna cewa Tinubu ya tsaya kan alkawarin da ya yi na ganin an gudanar da zaben cikin gaskiya, adalci da sahihanci.
Sai dai Olajengbesi ya ce duk da cewa zaben ya kasance sahihi, ba za a iya cewa ya kasance cikakke cikin ‘yanci da adalci ba, saboda wasu abubuwan danniya da aka samu.
Ya yi ikirarin cewa an kama wasu magoya bayan jam’iyyun adawa, inda ya ce sama da mutane 11 aka kama yayin gudanar da zaben.
Olajengbesi ya ce:
“Muna son mu kasance masu gaskiya da ku, muna kuma godiya ga shugaban kasa saboda tun farkon wannan zabe ya sanar da duniya, sannan ya ba INEC da dukkan hukumomin tsaro umarnin tabbatar da zaben cikin ‘yanci, adalci da sahihanci.
“Muna ganin wannan zabe sahihi ne, amma ba mu yarda cewa ya kasance cikin ‘yanci da adalci ba saboda an samu danniya. Mutanenmu har yanzu suna tsare.”

Source: Twitter
Tinubu ya sha yabo daga yan jam'iyyar Accord
Sai dai ya yaba wa shugaban kasar saboda ganin an bar tsarin zaben ya gudana, sannan aka mutunta sakamakon da aka samu.
Ya kuma bayyana cewa Shugaba Tinubu ya tuntubi Adeleke domin taya shi murnar nasara tun kafin a sanar da cikakken sakamakon zaben a hukumance.
Olajengbesi ya ce:
“Muna farin ciki cewa shugaban kasa ya tsaya kan abin da ya fada, ya kuma dage cewa dole ne a yi abin da ya dace.
“Bari in fada muku wannan cikin gaggawa: tun kafin a sanar da sakamakon a daren jiya, shugaban kasa ya kira gwamna ya taya shi murna, kuma wannan shi ne shugabanci nagari.”
A sakamakon da INEC ta sanar, Adeleke ya samu kuri’u 511,067, inda ya doke babban abokin hamayyarsa, Bola Oyebamiji na jam’iyyar APC, wanda ya samu kuri’u 444,815.
Umarnin Tinubu ga INEC kan zaben Osun
An ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci INEC ta yi amfani da zaben gwamnan Osun wajen nuna shirinta na babban zaben 2027.
Mai girma Bola Tinubu ya kuma umarci jami’an tsaro su tabbatar da an gudanar da zaben cikin lumana da gaskiya.
’Yan takara 15 ne za su fafata a zaben gwamnan Osun da za a gudanar ranar Asabar, 15 ga Agusta, 2026.
Asali: Legit.ng


