Ainihin Dalilin Gwamna Nasir Idris na Sauya Mataimakinsa a 2027

Ainihin Dalilin Gwamna Nasir Idris na Sauya Mataimakinsa a 2027

  • Gwamnan Kebbi, Nasir Idris, ya sauke mataimakinsa, Sanata Umar Abubakar Tafida, tare da maye gurbinsa da tsohon Kwamishinan Kudi, Ibrahim Muhammed Augie
  • Jam’iyyar APC mai mulki ta ce an dauki matakin ne bisa shawarar kwararrun lauyoyi, tare da amincewar mataimakin gwamnan da kansa
  • Masu sharhi na ganin matakin na da alaka da shari’ar da aka yi bayan zaben 2023 kan takardun shaidar karatun mataimakin gwamnan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – A ‘yan kwanakin da suka gabata ne Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya sauke mataimakinsa, Sanata Umar Abubakar Tafida.

Nan take kuma ya zabbi Ibrahim Muhammed Augie, tsohon Kwamishinan Kudi, a matsayin sabon abokin takararsa a zaben gwamnan jihar na 2027.

Gwamna Nasir Idris na hakura da mataimakinsa
Gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris Hoto: Sarki Yahaya
Source: Facebook

Rahoton da ya kebanta ga Daily Trust ya bayyana cewa an dade ana rade-radin sauya mataimakin gwamnan, inda ake cewa wasu mutane da suka hada da Samaila Biu da Ibrahim Muhammed Augie na cikin wadanda ake la’akari da su.

Kara karanta wannan

Abubuwan da ya dace a sani game da yarjejeniyar da aka yi tsakanin Musulmi da Kiristocin Najeriya

APC ta yi magana kan siyasar Kebbi

Sakataren yada labarai na jam’iyyar APC na kasa, Muhammed Suleiman Argungu, ya tabbatar da hakan yayin wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da aka gudanar a fadar shugaban kasa da ke Birnin Kebbi.

Argungu ya bayyana cewa an sauke Tafida ne daga matsayin abokin takarar Gwamna Idris a zaben 2027 bisa shawarar kwararrun lauyoyi.

APC ta ce babu matsala a tsakanin Nasir Idris da mataimakinsa
Taswirar jihar Kebbi a Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya kuma sanar da cewa Ibrahim Muhammed Augie shi ne sabon abokin takarar gwamnan a zaben 2027. A cewarsa, mataimakin gwamnan ya amince tare da fahimtar dalilin da ya sa aka maye gurbinsa da Augie.

Argungu ya ce:

“Babu wata rashin jituwar da ke tsakanin gwamna da mataimakin gwamna. Ina kira ga dukkan magoya bayan APC a fadin jihar da su ci gaba da kasancewa cikin hadin kai tare da yin aiki tare domin samun nasarar APC a zaben 2027 a Jihar Kebbi.”

Abin da Nasir Idris ya ce a Kebbi

Kara karanta wannan

MURIC ta zargi INEC da tilasta wa mata tube hijabi a zaben Osun

Gwamna Idris ya maimaita wannan matsaya, inda ya gode wa al’ummar Masarautar Argungu, daga inda mataimakinsa da aka sauke ya fito, bisa ci gaba da goyon bayan gwamnatinsa.

Ya ce babu wata rashin jituwa tsakaninsa da Tafida, yana mai cewa an sauya mataimakin gwamnan ne saboda wasu dalilai na shari’a, tare da fahimtar matakin da amincewar mataimakin gwamnan.

Duk da cewa gwamnan da sakataren yada labaran APC ba su bayyana cikakken bayani kan shawarar lauyoyin ba, wasu masu sharhi kan harkokin siyasa sun danganta matakin da shari’ar da aka yi bayan zaben 2023 kan takardun shaidar karatun mataimakin gwamnan.

A wancan lokaci, jam’iyyar PDP da dan takararta na gwamna, Manjo Janar Aminu Bande mai ritaya, sun garzaya kotun sauraron kararrakin zabe suna kalubalantar sahihancin takardar shaidar da Tafida ya gabatar wa INEC a shekarar 2015.

Lamarin ya kai har Kotun Koli, inda aka gabatar da shaidu da takardu kan halartar Tafida jarrabawar gwaji ta Kwalejin Malamai ta Sultan Abubakar.

Gwamna ya yi nade-nade a Kebbi

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan jihar Kebbi, Dr Nasir Idris, ya amince da kafa sabuwar gunduma mai kunshe da yankunan kauyuka takwas a karamar hukumar Dandi.

Kara karanta wannan

'Ina N4tr suka shiga"? Atiku ya kalubalanci Tinubu kan farfado da matatun mai

Dr. Nasir Idris ya kuma amince da nada sabon mai unguwa a karamar hukumar Augie domin karfafa tsarin mulkin gargajiya da inganta shugabanci a matakin kasa.

Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Sarauta, Alhaji Garba Umar Dutsinmari, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Birnin Kebbi ranar Alhamis, 13 ga watan Agustan 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng