FAAC Ta Cika Aljihun Gwamnatin Tinubu da Jihohi, an Raba Abin da ba a Taba Samu ba
- FAAC ta raba N3.007tn ga gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi a watan Yulin shekarar 2026
- Rabon watan Yuli shi ne mafi girma da aka taɓa rabawa tun bayan da Bola Tinubu ya zama shugaban ƙasa
- Gwamnatin tarayya ta samu kaso mafi tsoka a cikin kudaden yayin da jihohi da kananan hukumomi suka biyo baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Kwamitin raba kudin asusun tarayya (FAAC) ya ce gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi (LGAs) sun raba jimillar N3.007tn a watan Yulin 2027.
Adadin shi ne mafi girman rabon kuɗin da aka samu zuwa yanzu tun bayan da Shugaba Bola Tinubu ya hau mulki. A watan Yuni, FAAC ta raba N2.5tn ga matakan gwamnati.

Source: Twitter
Jaridar TheCable ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Bawa Mokwa, daraktan hulɗa da jama’a a ofishin babban akawun tarayya, ya fitar ranar Talata, 18 ga watan Agustan 2026.
A cewar sanarwar, kwamitin ya gudanar da taronsa a Owerri, jihar Imo, yayin taron Majalisar Ƙasa kan Tarayya da Ci gaban Tattalin Arziki (NACOFED) da ke gudana.
FAAC ta ce cikin jimillar kuɗin da aka raba, gwamnatin tarayya ta samu N1.14tn, jihohi sun samu N943.35bn, yayin da ƙananan hukumomi suka samu N673.64bn.
An kuma raba N243.47bn, wanda ya kai kashi 13 na kuɗin rabon arzikin ƙasa, ga jihohin da suka cancanci samun sa.
Kuɗin shiga sun ƙaru
FAAC ta kuma ce kuɗin shiga na doka gaba ɗaya ya tashi zuwa N4.35tn a watan Yuli, wanda ke nuna ƙarin N658.08bn ko kuma 17.8% daga N3.7tn da aka samu a watan Yuni.
Sai dai kuɗin shiga daga Harajin Ƙarin Darajar Kaya (VAT) ya ragu kaɗan zuwa N793.96bn daga N799.74bn da aka samu a watan Yuni, jaridar Tribune ta kawo labarin.
Kwamitin ya danganta ƙarin kuɗin shiga na doka da karuwar kuɗaɗen da aka samu daga harajin ribar man fetur (PPT), harajin sinadaran makamashin ƙasa (HT), harajin kuɗin shiga na kamfanoni (CIT), harajin ribar kadarori (CGT), harajin hatimi (SDT), kuɗaɗen haraji daga man fetur, kuɗaɗen haraji daga ma’adinai, harajin kaya da kuma tarar kona iskar gas.
FAAC ta ce raguwar kuɗaɗen VAT, harajin shigo da kaya, kuɗaɗen harajin Yarjejeniyar Harajin Waje ta Bai Ɗaya (CET), kuɗaɗen haya da suka shafi kona iskar gas da kuma sauran kuɗaɗen da ake samu daga man fetur sun ɗan rage tasirin ƙarin kuɗin shiga.

Source: Twitter
Batun karkatar da kudaden FAAC
A wani labarin kuma, Ma’aikatar kuɗi ta tarayya ta yi magana kan rahotannin kafofin yaɗa labarai da ke nuna cewa ana karkatar da kuɗaɗen shigar asusun tarayya ko kuma ana kashe kudin a ɓoye.
Ma'aikatar ta bayyana cewa waɗannan rahotanni sun yi mummunar fassara ga rahoton Bankin Duniya na baya-bayan nan game da ci gaban da Najeriya ta samu.
Asali: Legit.ng

