Iran Ta Dauko da Zafi, Ta Gargadi Makwabtanta kan Taimakon Amurka
- Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta gargadi kasashen da ke gabar Tekun Fasha kan taimakawa sojojin Amurka, tana mai cewa hakan zai zama kamar shiga aikin sojin Amurka
- Shugaban hafsoshin sojojin Iran Ali Abdollahi ya ce duk wani taimako ko saukaka wa sojojin Amurka zai zama shiga cikin ayyukan sojin Amurka
- Gargadin ya zo ne yayin da ake tura jirgin yakin USS George Washington zuwa Gabas ta Tsakiya domin maye gurbin USS Abraham Lincoln
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tehran, Iran - Rundunar sojojin Iran ta gargadi kasashen da ke gabar Tekun Fasha kan taimakawa sojojin Amurka.
Rundunar sojojin ta bayyana cewa duk wani taimako da aka ba su zai zama tamkar shiga cikin ayyukan sojin Amurka.

Source: Getty Images
Tashar Aljazeera ta kawo rahoton cewa shugaban hafsoshin sojojin Iran, Ali Abdollahi, ya bayyana hakan a ranar Laraba, 19 ga watan Agustan 2026.
Ali Abdollahi ya ce duk wani taimako ko saukaka wa sojojin Amurka da ake daukarsa a matsayin taimakon sojin Amurka zai zama shiga cikin aikin sojin Amurka, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Iran, Mehr, ya ruwaito.
Yakin Iran da Amurka
Yakin Iran da Amurka ya barke a ranar 28 ga Fabrairu bayan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Iran ta mayar da martani da hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuka, ciki har da hare-hare kan sansanonin sojin Amurka da ke fadin yankin.
Abdollahi ya ce ba kasafai ake ganin irin wannan adadi mai yawa na jiragen soji, musamman jiragen dakon mai, a sansanonin soji na yankin ba tare da kasashen da ke karbar su sun sani ba.
Ya ce kasashen da ke makwabtaka da Tekun Fasha, wadanda suka fitar da kalamai daban-daban cewa ba za su bar Amurka ta yi amfani da yankunansu wajen kai wa Iran hari ba, ya kamata su sani cewa Iran na sane da abin da ke faruwa.
An tura USS George Washington
Gargadin Iran ya zo ne yayin da ake sake tura jirgin yakin USS George Washington zuwa Gabas ta Tsakiya domin maye gurbin USS Abraham Lincoln.
Wannan mataki ya biyo bayan rahotannin da ke cewa yanayin rayuwar ma’aikatan USS Abraham Lincoln ya tabarbare.

Source: Twitter
Karanta wasu labaran kan yakin Amurka, Iran
- Yakin Iran ya shafa wa Trump kashin kaji, farin jininsa ya ragu sosai a Amurka
- An zo wajen: Trump ya fadi babban burin gwamnatinsa kan Iran
- Kasar musulunci ta Iran ta ba Amurka hanya mai sauƙi domin buɗe mashigar Hormuz
Trump ya yi barazanar kai wa Oman hari
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi barazanar kai wa kasar Oman hari wadda take kawa ce ga Amurka.
Shugaba Donald Trump ya yi wa Oman barazanar kai hari ne idan ta kawo cikas ga kokarin Washington na cimma yarjejeniya da Iran kan sarrafa zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz.
Trump ya yi barazanar cewa idan Oman ta yi katsalandan to tabbas Amurka za ta kai mummunan hari kan kasar.
Asali: Legit.ng

