Abubuwa 4 da Suka Sa ake Ganin Shugaban INEC ba zai Yi Adalci ba a 2027

Abubuwa 4 da Suka Sa ake Ganin Shugaban INEC ba zai Yi Adalci ba a 2027

'Yan Najeriya a bangarori da dama sun nuna shakku kan cewa shugaban hukumar zabe ta kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan zai masu adalci a 2027.

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban hukumar zabe ta kasa (INEC) Farfesa Joash Amupitan na fuskantar suka daga bangarori da dama a Najeriya.

Kungiyoyin addinin Musulunci da 'yan siyasa a Najeriya sun nuna shakku kan cewa da wahala ya iya masu adalci a zaben shugaban kasar da za a yi a 2027.

Shugaban hukumar INEC, Farfesa Joash Amupitan
Farfesa Joash Amupitan a ofishin hukumar zabe. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

A wannan rahoton, mun tattaro muku wasu dalilai da kungiyoyin addini da na siyasa ke gabatarwa game da nuna shakku kan adalcin Amupitan.

1. Zargin wariyar addini

Shugaban hukumar, INEC Farfesa Amupitan, ya fuskanci suka kan wata tsohuwar takarda ta koke da ya tura Amurka, inda aka ce ya nuna damuwa kan abin da ya kira kisan kiyashi ga Kiristoci a Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwammati ta kinkimo wa mutane aiki, bashin N724,000 ya hau kan kowane 'dan Najeriya

Wannan ya jawo suka daga ƙungiyoyi kamar Majalisar Ƙoli ta Harkokin Shari'ar Musulunci, wadda ta ce irin wannan ra’ayi na iya jefa shakku kan adalcinsa a ƙasa mai yawan addinai daban-daban, tare da kiran a cire shi daga muƙaminsa.

Farfesa Bashir Aliyu Umar daga daga majalisar Shari'ar Musulinci da Farfesa Ishaq Akintola na kungiyar MURIC sun nuna cewa ba su gamsu da cewa Amupitan zai yi adalci ba.

Farfesa Bashir Aliyu Umar
Farfesa Bashir Aliyu yana wa'azi a Kano. Hoto: Dr Bashir Aliyu Umar
Source: Facebook

Bisa zargin nuna wariyar addini, shugaban majalisar malaman kungiyar Izala, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya fito ya nemi a sauya shugaban INEC.

2. Rikicin jagorancin jam'iyyar ADC

Punch ta wallafa cewa shugaban INEC ya cire sunayen David Mark da Rauf Aregbesola a matsayin shugaba da sakatare na jam’iyyar ADC biyo bayan hukuncin kotu.

An ce cire sunayensu daga shafin hukumar INEC na iya raunana damar jam’iyyar wajen tsayar da ‘yan takara, lamarin da ya sanya wasu ke zargin yana yiwa APC aiki.

Yan ADC yayin zanga-zangar adawa da shugaban INEC
Shugabanni da jagororin INEC suna zanga-zangar adawa da shugaban INEC a Abuja. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Kakakin jam'iyyar ADC na kasa, Bolaji Abdullahi ya yi kira ga gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta sauke Amupitan saboda zargin cewa ba zai masu adalci a zabe ba.

Kara karanta wannan

Bayan tafiyar jami'an Amurka, 'yan ta'adda sun tsara kai babban hari Abuja, Neja

3. Batun sake tantance masu zaɓe

Wani babban batu da ya ya jawo shafawa Amupitan kashin kaji shi ne shirin sake tantance masu zaɓe da a yanzu haka aka ce an dakatar da shi.

Mutane da dama sun ce yunƙurin sake tantance miliyoyin masu zaɓe cikin ɗan lokaci kaɗan na iya hana ‘yan Najeriya da dama damar kaɗa ƙuri’a a zaɓen 2027.

Wani matashi na kada kuri'a a zaben Abuja
Mai kada kuri'a a zaben kananan hukumomi da aka yi a Abuja. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Lamarin ya jawo suka ga shugaban INEC daga malamai tare da zargin cewa yana yi wa APC da shugaba Bola Tinubu aiki ta bayan fage kuma ba zai masu adalci ba.

4- Zargin goyon bayan APC a X

An kuma tayar da tambayoyi kan wani asusun sada zumunta na X da ake dangantawa da Amupitan, wanda aka ce yana ɗauke da rubuce-rubuce masu goyon bayan APC da kuma sukar ƙungiyoyin adawa kamar “Obidient.”

Duk da Amupitan ya musanta mallakar akawun, wasu bayanai a yanar gizo na nuna alaƙa da wasu bayanan sirri kamar adireshin imel da lambar waya, wanda ya sa batun ya ci gaba da kasancewa cikin ce-ce-ku-ce.

Kara karanta wannan

Atiku ya haƙura da neman mulkin Najeriya, ya faɗi lokacin ƙarshe na yin takara

Farfesa Joash Amupitan a ofisihin INEC
Farfesa Joash Amupitan yayin tattaunawa da jami'an INEC a Abuja. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

A wani sako da ya wallafa a Facebook, Farfesa Farouk Kperogi ya bayyana cewa hakan zai sanya mutane shakku kan ko Amupitan zai iya yi wa sauran jam'iyyu adalci.

Dalung ya zargi shugaban INEC

A wani labarin, kun ji cewa tsohon ministan wasannin Najeriya, Barista Solomon Dalung ya zargi shugaban INEC da rashin adalci.

Dalung ya yi zargin cewa akwai abubuwa marasa dadi da kuma na rashin gaskiya da Farfesa Joash Amupitan ya yi a jami'ar Jos a shekarun baya.

Saboda haka Dalung ya ce korafin da INEC ta yi game da jam'iyyar adawa ta ADC ba shi da tushe face barazana da neman razana su.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng