Abubuwan da 'Yan Najeriya Za Su Gani idan Jam'iyyar ADC Ta Kifar da Tinubu a Zaben 2027
- Sanata Aminu Waziru Tambuwal ya jero fannonin da ADC za ta maida hankali idan ta karbi mulkin Najeriya a zaben 2027
- Tambuwal ya bayyana cewa gwamnatin ADC za ta share hawayen 'yan Najeriya dangane da matsalar tsaro, noma da rashin ayyukan yi
- Tsohon gwamnan na jihar Sokoto ya kuma tabo batun rikicin da ADC ka iya fuskanta wajen tsaida 'dan takarar shugaban kasa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina, Nigeria - Tsohon gwamnan Sokoto kuma jagoran ADC a jihar, Sanata Aminu Tambuwal, ya bayyana manyan abubuwan da ‘yan Najeriya za su sa rai idan jam’iyyar ta karɓi mulkin ƙasa a 2027.
Tambuwal ya yi wannan bayani ne ga manema labarai bayan kammala taron ADC a matakin jiha, inda ya jaddada cewa tsaro shi ne babban abin da za su fi bai wa muhimmanci.

Source: Twitter
Jam'iyyar ADC za ta magance matsalar tsaro
A cewarsa, babu wani ci gaba mai ma’ana da zai samu idan ba a magance matsalar tsaro ba, kamar yadda jaridar Tribune Nigeria ta ruwaito.
Tambuwal ya ce gwamnatin ADC za ta ɗauki matakai na zamani, fasaha da kuma haɗin gwiwar al’umma domin shawo kan matsalar tsaro a sassan kasar nan gaba daya.
Ya ƙara da cewa bangaren tattalin arziki zai kasance a sahun gaba, musamman wajen rage wahalhalu, yaƙi da rashin aikin yi ga matasa, da kuma samar da dama ta hanyar ƙirƙirar ayyukan yi, tallafawa ƙananan da matsakaitan sana’o’i.
Tambuwal ya jero fannoni masu muhimmanci
Tambuwal ya ce ilimi da noma za su zama ginshiƙai masu muhimmanci a manufofin jam’iyyarADC, inda ya jaddada buƙatar saka hannun jari mai ɗorewa a ilimi domin samar da cigaba na dogon lokaci.
Ya bayyana cewa noma ne babbar damar Najeriya wajen samar da wadataccen abinci da kuma ayyukan yi idan aka tsara shi yadda ya kamata.

Kara karanta wannan
Saraki ya jefi gwamnatin Buhari da zargi kan fashin Offa, ya fallasa gwamnan Kwara
Haka kuma, ya nuna cewa wutar lantarki na daga cikin muhimman fannoni da za su maida hankali a kai, yana mai cewa samar da ingantacciyar wuta zai taimaka wajen bunƙasa masana’antu da kuma ƙara ƙarfin tattalin arziki.
Ya ce manufar jam’iyyar ADC gaba ɗaya ita ce gina gwamnati mai sauraro, mai gaskiya, wadda za ta mayar da hankali wajen inganta rayuwar ‘yan ƙasa.
Yadda ADC ta shirya fitar da dan takara
Tambuwal ya kuma yi magana kan yiwuwar rikice-rikicen cikin gida a ADC musamman dangane da neman takarar shugaban ƙasa, inda ya ce irin wannan abu na cikin tsarin dimokuraɗiyya.

Source: Facebook
Ya ce jam’iyyar za ta bi hanyoyin dimokuraɗiyya, inda za a nemi cimma matsaya gudata hanyar masalaha ko kuma a gudanar da zaɓen fitar da gwani idan hakan bai yiwu ba.
A ƙarshe, ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa gaskiya, adalci da haɗin kai za su taimaka wajen ƙarfafa jam’iyyar ADC maimakon raunana ta, kamar yadda tashar Channels tv ta kawo.
ADC ta fadi fargabar da Tinubu ke ciki
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta bayyana cewa kalaman Shugaba Bola Tinubu na cewa ba za a iya tsorata shi ba alamun nuna fargaba ne tun yanzu.

Kara karanta wannan
Shari'a ta dawo sabuwa: Saraki da tsohon gwamnan Kwara za su gurfana a kotu kan fashin Offa
A cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar, ta bayyana cewa kalaman shugaban suna nuna tsantsar fargaba da damuwa ne maimakon kwarin gwiwar da yake nuna wa a fili.
A cewar jam'iyyar ADC, akwai dalilai da dama da ya kamata su jefa shugaban ƙasa a cikin tsoro kafin babban zaɓen 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
