Rikicin ADC: Da Gaske an Kona Gidan Nafiu Bala a Gombe? An Samu Gaskiya

Rikicin ADC: Da Gaske an Kona Gidan Nafiu Bala a Gombe? An Samu Gaskiya

  • ’Yan sandan jihar Gombe sun yi ƙarin haske kan jita-jitar cewa an kona gidan Nafiu Bala Gombe wanda ake zargi da jawo rikicin ADC
  • Rundunar ta ƙaryata rahoton da ke cewa an kona gidan shugaban tsagin ADC da ake yaɗawa a kafofin sadarwa
  • Kwamishinan ’yan sanda, Umar Ahmed Chuso ya bukaci jama’a su yi watsi da rahoton, yana tabbatar da cewa zaman lafiya da tsaro suna nan a Gombe

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Nassarawo, Gombe - Rundunar ’yan sandan Gombe ta fayyace gaskiyar abin da ake yaɗawa game da kona gidan shugaban tsagin ADC.

Rundunar ta musanta rahotannin da suka bazu a shafukan sada zumunta cewa an kona gidan Nafiu Bala a jihar.

Yan sanda sun yi magana kan zargin kona gidan Nafiu Bala
Kakakin rundunar ƴan sanda a Gombe, Buhari Abdullahi. Hoto: Buharee Abdullahi Dam Roni.
Source: UGC

Hakan na cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook a daren yau Alhamis 30 ga watan Afrilun 2026.

Kara karanta wannan

Mark da Nafi'u Gombe: Kotun Koli ta yanke hukunci kan rikicin shugabancin ADC

Kotun koli ta yi hukunci kan rikicin ADC

Wannan jita-jita na zuwa ne a ranar da Kotun Koli ta yanke hukuncin karshe game da rikicin shugabancin jam'iyyar ADC.

Matashin 'dan siyasa, Nafiu Bala daga Gombe shi ke kalubalantar bangaren David Mark a matsayin shugaba wanda suke korafi a kotu.

Daga bisani, kotun ta tabbatar da sahihancin bangarensu David Mark bayan fatali da korafin tsagin Nafiu Bala.

Martanin yan sanda kan 'kona' gidan Nafiu Bala

Rundunar ta bayyana labarin a matsayin karya da yaudara inda ta shawarci al'umma su guji yaɗa labarin.

Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana haka inda ya ce rundunar ba ta samu wani rahoto makamancin haka ba.

Wakilinmu ya ruwaito cewa Nafiu Bala ya ayyana kansa a matsayin shugaban tsagin adawa na jam’iyyar ADC ne wanda ya jawo maganganu a Najeriya.

Wani sako da ya bazu a kafofin sadarwa ya yi zargin wasu fusatattun mutane sun kona gidansa.

Kara karanta wannan

Shaidan sojoji ya fasa kwai a kotu, ya fadi yadda aka shirya yi wa Tinubu juyin mulki

Yan sanda sun karyata labarin kona gidan Nafiu Bala a Gombe
Kakakin rundunar ƴan sanda a Gombe, Buhari Abdullahi da shugaban tsagin ADC, Nafiu Bala. Hoto: Buharee Abdullahi Dam Roni, Hon. Nafiu Bala.
Source: Facebook

Tabbacin da ƴan sanda suka bayar

Sai dai kakakin yan sanda, ya ce rundunar ta tabbatar da cewa rahoton ba gaskiya ba ne, ya ce babu wani wuri a Gombe da aka samu aukuwar irin wannan lamari.

“Rundunar ta tabbatar da cewa rahoton karya ne, domin babu wani irin al’amari da aka samu a ko’ina cikin jihar."

- In ji Buharee Abdullahi

Kwamishinan ’yan sanda na jihar, CP Umar Ahmed Chuso, ya bukaci jama’a su yi watsi da bayanan bogi tare da kwantar da hankulansu.

Ya tabbatar da cewa rundunar tana ci gaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin Gombe domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Ya ce:

“Kwamishinan ’yan sanda na jihar Gombe, CP Umar Ahmed Chuso, yana kira ga jama’a su yi watsi da wannan bayanin karya tare da kwantar da hankulansu."

Rikicin ADC: Nafiu Bala ya caccaki Kwankwaso

A wani rahoton, mun ba ku labarin cewa jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta samu kanta cikin rikicin shugabanci da ya ki ci ya ki cinyewa a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Kotu ta bada umarni kan jami'in DSS da ake zargi ya sace budurwa a Jigawa

Shugaban tsagin ADC na kasa, Nafiu Bala Gombe, ya yi zarge-zarge kan Sanaga Rabiu Musa Kwankwaso wanda ya shigar jam'iyyar.

Nafiu Bala ya nuna cewa Kwankwaso ya taka rawar gani wajen hana dan Arewa yin nasara a zaben shugaban kasa na 2023.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.