Kotu Ta Rikita Lissafin 'Yan Adawa, Ta Hana INEC Amincewa da Tarukan Jam'iyyar ADC
- Babbar kotun tarayya ta soke babban taron ADC na kasa, kuma ta hana hukumar zaben Najeriya (INEC) anincewa da shi
- A hukuncin da Mai Shari'a Joyce Abdulmalik ta yanke yau Laraba, ta ce tana da hurumin tsoma baki kan harkokin jam'iyyu idan suka karya doka
- Kotun ta kuma hana INEC amincewa ko shiga tarukan da tsagin David Marka zai shirya a matakin jihohi saboda wa'adin shugabanni masu ci bai kare ba
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta hana Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) amincewa ko shiga duk wani taro da shugabancin rikon kwarya na jam’iyyar ADC suka shirya a matakin kasa da jihohi.
Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta ta babbar kotun mai zama a Abuja ce ta yanke wannan hukunci a yau Laraba, 29 ga watan Afrilun 2026.

Source: Twitter
A rahoton Leadership, alkalin ta kuma hana tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, da wasu jiga-jigan ADC tsoma baki cikin ayyuka da wa’adin shugabannin jam'iyya jihohi da aka zaba.
Rikicin ADC ya dauki zafi
Hukuncin ya kara tsananta rikicin shugabanci da ke addabar jam’iyyar ADC, wanda kuma zai yi tasiri kan yadda za a tafiyar da harkokin jam’iyyar nan gaba.
Wadanda suka shigar da kara sun ce shugabancin rikon kwarya da aka nada karkashin jagorancin Sanata David Marki, ba shi da hurumin gudanar da tarukan jihohi ko kafa kwamitin da zai yi hakan.
Sun jaddada wa kotu cewa shugabannin jam'iyya na kasa da aka zaba bisa kundin tsarin ADC ne ke da ikon shirya tarukan jihohi.
Shin kotu na da hukumim tsoma baki?
Mai shari’ar ta ce dole ne jam’iyyun siyasa su bi ka’idojin dimukuraɗiyya da kundin tsarin mulkin da suka kafa da kansu.
Ta ce kotu na da hurumin shiga cikin irin wannan lamari idan aka samu karya doka ko kundin tsarin mulki, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Hukuncin da kotu ta yanke
Kotun ta tabbatar da cewa wa’adin shugabannin jihohi na jam’iyyar ADC bai kare ba, kuma za su ci gaba da jagoranci har zuwa karshen lokacin da doka ta tanadar masu.
Ta kuma soke kwamitin da aka kafa domin shirya tarukan, sannan ta hana hukumar INEC amincewa da duk wani taro da wannan kwamitin zai gudanar.
Haka kuma ta hana wadanda ake kara shirya taro ko daukar matakin da zai kawo cikas ga shugabannin jihohi na jam’iyyar ta ADC.

Source: Facebook
Yan adawa za su tsaida dana takara 1 a 2027
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyun adawa sun gudanar da babban taro a birnin Ibadan domin tattauna batutuwan da suka shafi siyasar kasar nan.
Manyan jagororin adawar kasar nan sun amince za su fitar da dan takarar shugaban kasa guda daya da zai gwabza da Shugaba Tinubu a zaben 2027.
Manyan jiga-jigan adawa da suka haɗa da Atiku Abubakar, Rabiu Musa Kwankwaso , Rotimi Amaechi, Peter Obi da Rauf Aregbesola, sun halarci taron.
Asali: Legit.ng

