Mahaifin Davido ya Ambaci ministan Tinubu da Ya Yaki Tazarcen Gwamna Adeleke
- Dr Adedeji Adeleke ya yi murna cewa nasarar da dan uwansa ya samu amsa ce ta addu'o'in da suka rika yi
- Attajirin ya zargi Oyetola da kokarin hana dan uwansa, Gwamna Ademola Adeleke, yin nasara a zaben Osun
- Yayan gwamnan ya ce sun fuskanci mummunar kiyayya da siyasa saboda minista yana so APC ta koma mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Osun - Babban mai kudi kuma yayan gwamnan Osun, Adedeji Adeleke, ya fadi abin da ya sani kan zaben da aka yi kwana nan.
Adedeji Adeleke ya zargi tsohon gwamnan jihar Osun da yin duk abin da zai iya wajen ganin bayan mulkin Ademola Adeleke.

Source: Twitter
An jefi tsohon gwamnan Osun da muguwar siyasa
Attajirin ya zargi Ministan kula da arzikin teku, Adegboyega Oyetola da yakar tazarcen Ademola Adeleke a haukace in ji Leadership.
Masoya gwamnan Osun sun shirya liyafa domin nuna farin cikin lashe zabe, a nan ne aka ji attajirin ya yi wadannan maganganu.
Adedeji Adeleke ya jefo zargin da suka yi kama da ‘dan sa wato Davido, wanda ya ce APC ta kashe N110bn domin ta karbe mulki.
Tsohon gwamnan wanda yanzu minista ne, ya goyi bayan takarar Oyebamiji a APC, amma a karshe ya tashi da kuri’u 444,815.
Addu'o'in da Adedeji Adeleke ya rika yi
Mahaifin mawakin ya ce ya yi addu’a saboda irin adawar da ya ga an nuna wa kaninsa wanda ya nemi tazarce a jam’iyyar Accord.
A karshe kuwa ya ce Ubangiji ya amsa addu’o’in da ya yi gabanin zaben gwamnan, aka ga bayan ‘yan adawa duk da sun fi karfi.
Ya zargi ‘yan APC da nuna masa bakar kiyayya tare da neman mulki ido a rufe - babu ruwansu ko mutane za su mutu ko za su rayu.
“Amma Ubangiji ya nuna masu iyaka. Yanzu sun san Ubangiji guda ne kuma babu wani ‘dan adam mai karfi sai Shi.
A duk mako ina yin azumin kwanaki biyu domin Shi, kuma na roki Ubangiji ya taimake shi (gwamna). Adawar ta yi yawa.
- Dr Adedeji Adeleke

Source: Facebook
An rahoto cewa da yake jawabi a Ede, ya yi kira ga magoya baya su cigaba da yi wa gwamnan addu’a.
Da aka nemi jin ta bakin Ministan albarkacin tekun domin maida martani kan wannan zargi, ‘yan jarida ba su same shi ba.
Magoya baya sun so Oyetola ya sake takara
Ana da labarin kungiyar magoya bayan APC (IPSC) ta so a ce ministan tarayya, Adegboyega Oyetola ya ajiye mukaminsa, ya sake fitowa takara.
Kungiyar ta bayyana cewa tsayawar Oyetola kawai ce zata hana rabuwar kai a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar APC tare da tabbatar da haɗin kan kowa.
A zaben 2022 lokacin yana jam'iyyar PDP, Ademola Adeleke ne ya doke Gboyega Oyetola da ya nemi ya zarce a matsayin gwamna a jihar Osun.
Asali: Legit.ng

