Mutuwa Mai Yankar Kauna: An Shirya Maye Gurbin Dan Majalisar Tarayya da Ya Rasu

Mutuwa Mai Yankar Kauna: An Shirya Maye Gurbin Dan Majalisar Tarayya da Ya Rasu

  • Hukumar INEC ta sanya Asabar, 19 ga Satumba, 2026, domin gudanar da zaɓen cike gurbi a mazabar Gombe/Kwami/Funakaye
  • Za a gudanar da zaɓen ne bayan rasuwar ɗan majalisar wakilai mai wakiltar wannan mazaba ta jihar Glmbe, Yaya Bauchi Tongo
  • Jam’iyyun siyasa za su gudanar da zaɓukan fidda gwani daga 21 zuwa 25 ga Agusta, 2026 kafin lokacin zaben

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Gombe, Nigeria - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanya Asabar, 19 ga Satumba, 2026, domin gudanar da zaɓen cike gurbin kujerar dan majalisar wakailai na mazabar Gombe/Kwami/Funakaye.

Ofishin INEC na Jihar Gombe ne ya bayyana hakan ranar Talata, 18 ga watan Agusta, 2026 a cikin jadawalin lokacin da ayyukan da za a gudanar gabanin zaɓen.

INEC.
Tambarin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

Rahoton Leadership ya nuna cewa zaɓen ya zama dole ne bayan rasuwar dan Majalisar wakilan tarayya na mazabar, Hon. Yaya Bauchi Tongo, wanda ya rasu a watan Yuni bayan gajeruwar rashin lafiya.

Kara karanta wannan

FAAC ta cika aljihun gwamnatin Tinubu da jihohi, an raba abin da ba a taba samu ba

INEC ta fitar da jadawalin zaben

Hukumar INEC ta ce za a gudanar da zaɓen bisa Sashe na 76(2) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, wanda aka yi wa kwaskwarima, da kuma tanade-tanaden Dokar Zaɓe.

Hakan dai na kunshe a cikin wata sanarwa mai ɗauke da kwanan watan 17 ga Agusta, wadda jami’in hulɗa da jama’a na INEC, Mohorret Bigun, ya sanya wa hannu a madadin Kwamishinan Zaɓe na Jihar Gombe, Umar Mukhtar Gajiram,

A jadawalin da INEC ta tsara, jam’iyyun siyasar da ke son shiga zaɓen za su gudanar da zaɓukan fitar da gwani tsakanin 21 da 25 ga Agusta, 2026.

Yaushe za a fara kamfe?

Hukumar ta ce za a wallafa jerin sunayen ’yan takarar da aka tsayar ranar 8 ga Satumba, sannan za a fara yaƙin neman zaɓe ranar 9 ga Satumba, wanda zai ƙare ranar 17 ga Satumba, kwana biyu kafin gudanar da zaɓen.

Kara karanta wannan

Akwai kura: INEC ta lissafo abubuwan da ke barazana ga zaben 2027

INEC ta buƙaci jam’iyyun siyasa su bi jadawalin da aka fitar tare da gudanar da dukkan ayyukansu bisa tanade-tanaden doka.

Yaya Bauchi Tongo.
Marigayi tsohon dan majalisar wakilai daga Gombe, Yaya Bauchi Tongo Hoto: Rabiu B. Goro
Source: Facebook

INEC ta yi alkawarin adalci

Hukumar ta tabbatar wa masu ruwa da tsaki a ƙananan hukumomin uku da ke cikin mazabar, waɗanda ke da rumfunan zaɓe 903, cewa za ta samar da dama daidai ga dukkan masu fafatawa.

INEC ta kuma yi alƙawarin gudanar da zaɓe cikin ’yanci, adalci da kuma ba tare da nuna wariya ba, cewar rahoton Daily Post.

Hukumar ta ƙara kira ga masu kaɗa ƙuri’a da suka cancanta da su shiga cikin harkokin zaɓen tare da sauke nauyin da ke kansu na zama ’yan ƙasa.

INEC za ta dauki ma'aikatan wucin gadi

A wani labarin, kun ji cewa hukumar zaben Najeriya watau INEC ta ce za ta dauki kusan ma’aikatan wucin gadi miliyan 1.4 a babban zaɓen 2027.

Shugaban INEC , Farfesa Joash Amupitan, ya ce za a tura ma’aikatan wucin gadin zuwa rumfunan zaɓe sama da 176,000 da ke faɗin ƙasar nan

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262