Jorge Messi, mahaifin Lionel Messi kuma wakilinsa na dogon lokaci, ya rasu yana da shekaru 68 bayan fama da rashin lafiya na tsawon lokaci a Argentina.
Jorge Messi, mahaifin Lionel Messi kuma wakilinsa na dogon lokaci, ya rasu yana da shekaru 68 bayan fama da rashin lafiya na tsawon lokaci a Argentina.
Hukumar SMEDAN ta sake bude shirin tallafin N50,000 ga kananan 'yan kasuwa ns kyauta, amma masu anfani dole ne su dauki akalla ma'aikaci daya aiki.
Da wuya a samu wanda ya tashi ba tare da sha'awara tara da dukiya ba kuma dai Hausawa na cewa arziki kashi ne, a yayin da an samu wasu mashahuran kananan yara a Najeriya da suka tako shi tun kafin su kai shekarun samartaka.
Kwamishinan ya kara da cewa sojan kadai jami'an 'yan sanda suka samu, sanye da kakinsa, a wurin da motar ta yi hatsari. Bayan jami'an 'yan sanda sun binciki motar ne sai suka ga kananan buhunhunan tabar wiwin makare a cikinta
Rassan kungiyar kwadagon guda uku bayan wani taron gaggawa da ta gudanar a ranar Talata, ta ce ba ta da hannu a sanarwar da sakataren gwamnatin jihar ya gabatar dangane da fara biyan ma'aikatan jihar mafi karancin albashi.
Sauro ne yake dauke da kwayar cutan shawara kuma ana kamuwa da ita ta hanyar cizon sauron. Haka zalika cutar shawara , ana iya maganceta ta hanyar rigakafi kuma tana yaduwa ne ta hanyar cizon sauron kadai.
Tsohon kocin tawagar kwallon kafar Najeriya ya ce ya zuwa yanzu, sawun wadanda suka yi garkuwa da mahaifiyarsa ya bace wa jami'an 'yan sanda ta yadda sun gaza sanin makamar da za su rika domin fara bincike.
Wata mata dake zaune a garin Ibadan mai suna Esther Isaiah, ranar Larabar nan ta zargi mijin mahaifiyarsu mai suna John Dickson, da yi mata fyade ita da kanwarta. Da take sanar da hakan a wata kotu dake Mapo a garin na Ibadan...
Na kula cewa ba yarinya nake koma wa ba, kuma gashi mahaifiyar mijina ta fara tsangwamata tana cewa ina cin kudin dan ta ba tare da haifa masa komai ba. Daga baya ta zo ta fara zargin cewa na girme shi, ina yi masa wayo. "Lamarin
Wani dan Najeriya mai suna Haruna Moda Maina Asaga ya nuna alhini akan mutuwar kannasa guda biyu. Mutumin ya yayi rashi na kaninsa da kuma kanwarsa, Usman da Asha Modu Mai a, a Maiduguri, jihar Borno.
Kasar Isra'il ta kira wani yaro dan karamin yaro dan shekara hudu Musulmi dan kasar Palastine daga yankin Gabashin Jarusalam, domin binciken shi. Yaron mai suna Muhammad Rabi Elayyan wasu jami'an 'yan sanda ne masu yawan gaske...
Labarai
Samu kari