Akwai Matsala: Sababbin Bayanai Sun Fito kan Yadda Aka Tura Makudan Kudi a Asusun Atiku
- Atiku Abubakar ya nuna damuwa kan wasu makudan kudin da aka tura cikin asusun bankinsa ba tare da izininsa ba
- An bayyana kudin a matsayin 'kudin tallafin kamfe', duk da cewa Atiku bai nemi ko amince a tura masa kudin ba
- Bankin da aka tura kudin ya fara bincike, yayin da bayanai suka nuna cewa kudin ya fito ne daga wani asusun OPay
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Sabbin bayanai na kara fitowa kan dalilin da ya sa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ke matukar damuwa kan kudin da aka tura cikin asusunsa na banki ba tare da izininsa ba.
Ana fargabar cewa wannan kudi na iya zama wani yunkuri na danganta dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku da wasu mutane ko ayyukan da bai san komai a kansu ba.

Kara karanta wannan
Bincike kan shirin yi wa Tinubu juyin mulki ya rutsa da fitaccen jarumin fim a Najeriya

Source: Facebook
Vanguard ta tattaro cewa baya ga kudin da aka tura ba tare da an nemi izini ba, akwai damuwa kan wanda ya aika kudin da kuma dalilin yin hakan.
Atiku, ta bakin mai magana da yawunsa, Phrank Shaibu, ya bayyana damuwa bayan gano kudin, yana mai cewa tsohon mataimakin shugaban kasar da kungiyarsa ta siyasa ba su nemi tallafin kudin ba.
Shaibu ya ce:
“Ba Mai Girma tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ba, kuma ba kungiyarsa ta yakin neman zabe ce ta nemi, ta amince ko kuma ta san mutumin ko wata hukuma ta tura masa kudin ba."
Ana fargabar kudin na iya jawo zargi
Sai dai an gano cewa daya daga cikin manyan abubuwan da ke damun tawagar Atiku shi ne yiwuwar amfani da kudin wajen samar da wata alaka ta kudi tsakanin tsohon mataimakin shugaban kasar da wasu mutane ko ayyukan da ba shi da hannu.
Akwai fargabar cewa kudaden da ba a san asalinsu ba na iya jefa wanda aka tura wa kudin cikin tambayoyi kan yiwuwar alaka da ayyukan ta'addanci, safarar miyagun kwayoyi, damfara ko wasu laifuka.
Sai dai a halin yanzu, babu wata shaida da ke nuna cewa kudin ya fito daga wata kungiyar ‘yan ta’adda, masu safarar miyagun kwayoyi ko wata kungiyar masu aikata laifuka.
Damuwar ita ce yiwuwar karbar kudin da ba a bayyana asalinsa ba na iya haifar da matsala ko kuma a yi amfani da mu’amalar wajen samar da wata alaka mai illa ga suna da martabar Atiku.
Ta yaya aka samu bayanan asusun Atiku?
Wani abin da ke kara damun Atiku shi ne yadda wanda ya tura kudin ya samu bayanan asusunsa na banki tun farko.
A cewar sanarwar da Shaibu ya fitar a baya, asusun da aka tura kudin na kashin kansa ne, kuma ba a bayyana bayanansa ga jama'a.
Sanarwar ta ce:
“Asusun na kashin kansa ne kuma ba a samun bayanansa a bainar jama'a. Wannan ya haifar da muhimmiyar tambaya: Ta yaya wasu mutanen da ba a san su ba suka samu bayanan sirrin bankin wani dan kasa?”
Saturday Vanguard ta tattaro cewa akwai damuwa kan yiwuwar an fallasa bayanan asusun, wadanda a ka’ida bankin da hukumomin kula da harkokin kudi ne kadai ke iya samun su a yayin gudanar da ayyukansu na doka.

Kara karanta wannan
2027: Babban jigon APC a Arewa ya tada rigima, ya ce ba zai sake tallata Tinubu ba
Saboda haka, tawagar Atiku ta fara tambayar ko wani mutum da ke da damar shiga bayanan sirrin harkokin kudi ne ya fallasa bayanan asusun.

Source: Facebook
Banki ya fara bincike
Bankin da abin ya shafa, wanda yana cikin manyan bankunan Najeriya guda biyar, ya fara bincike kan yadda aka gudanar da wannan mu’amalar kudi.
Ana sa ran bankin zai sanar da Atiku sakamakon binciken a karshen mako, yayin da ake kokarin gano yadda mu’amalar ta faru da kuma, mafi muhimmanci, ko za a iya gano tushen kudin.
Atiku ya nemi Tinubu ya saki El-Rufai
Kun ji cewa Atiku Abubakar ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya umarci ICPC ta saki Nasir El-Rufai idan har yana iya ba EFCC umarni.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce umarnin da Tinubu ya ba EFCC ya karya ikirarin cewa hukumomin yaki da cin hanci suna aiki ba tare da katsalandan ba.
Asali: Legit.ng
