An kuma: An kara hantarar wani gwamnan Najeriya a kasar waje

An kuma: An kara hantarar wani gwamnan Najeriya a kasar waje

- Wasu masu zanga-zanga a birnin New York sun tozarta gwamnan jihar Edo, Gabriel Obaseki

- Gwamnan dai ya je birnin ne tare da wasu jami'an gwamnatin Najeriya don halartar taron majalisar dinkin duniya

- Koda masu zanga-zangar suka fara jifansa da miyagun kalamai, bai ko bi ta kansu ba

Wasu fusatattun masu zanga-zanga sun tozarta gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo.

An hantari gwamnan ne a yayin da yaje taron majalisar dinkin duniya da wasu jami'an gwamnati kamar yadda wani faifan bidiyo da Lindaikeji's Blog ya wallafa.

Masu zanga-zangar sun hango gwamnan ne a tafiya a wajen majalisar dinkin duniya da ke birnin New York.

An ji masu zanga-zangar na ihun "Obaseki barawo, ka fadi, a nan kaga tituna masu kyau".

KU KARANTA: 'Yan sanda sun gano gawarwaki cikin manyan kaburbura a Benue

Gwamnan jihar Edo din ya yi kamar na da shi suke na inda ya cigaba da maganarsa da wani mutum.

Idan zamu tuna a kwanakin baya, tsohon mataimakin majalisar dattawan Najeriya, Ekweremadu ya sha kashi a kasar Jamus.

Hakan kuwa ya sanya tsoro da fargaba matuka a zuciyoyin jiga-jigan 'yan siyasa kudancin kasar nan. Har ta kai ga basu sha'awar fita kasashen ketare shakatawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel