Mafi karancin albashi: Kungiyar Kwadago ta yi watsi da fara biyan N30,000 a jihar Kebbi

Mafi karancin albashi: Kungiyar Kwadago ta yi watsi da fara biyan N30,000 a jihar Kebbi

Rahotanni sun kawo cewa kungiyar kwadago reshen jihar Kebbi, ta yi watsi tare da nuna rashin amincewa da fara shirin biyan mafi karancin albashi na N30,000 da gwamnatin jihar ta yi sanarwa za a fara daga karshen wannan wata na Satumba.

Shugaban Kungiyar na Jihar Kebbi, Umar Halidu ne ya sanar da hakan ga manema labarai a ranar Labara, 25 ga watan Satumba bayan tashin da suka yi daga wani taron gaggawa.

A cewar Halidu sun ki amincewa da fara biyan sabon albashin ne bayan taron da suka gudanar tare da wakilan mambobin su na dukkan kananan hukumomin jihar guda 21.

Ya ce gwamnatin jihar Kebbi ba ta tuntube su ba, domin jin adadin kudaden da aka kara wa masu matakin albashi daga na 07 zuwa sama.

Ya ce ita dai gwamnatin tarayya abin da ta ce shi ne za a maida mafi karancin albashi daga naira 18,000 zuwa 30,000. Kuma masu wannan adadi kananan ma’aikata ne masu masu matakin albashi daga na 01 zuwa na 06.

Ya nuna mamakin yadda gwamnatin jihar ba ta tuntubi kungiyar kwadago ba domin zaman tattauna abin da za a kara wa masu matakin albashi daga na 07 zuwa sama.

Halidu ya ce gwamnatin Kebbi ita kadai ta yi kidan ta, kuma ta yi rawar ta. Don haka ba za su yarda ko amince da duk wani ‘yar burum-burum da za a yi wa ma’aikatan jihar ba.

KU KARANTA KUMA: Sheikh Pantami yayi bayani akan sabuwar gaisuwar zamani da ya kirkira da mata

A kan haka ne ya ce ba su amince da tsarin karin da aka shigo da shi ba, domin ba a yi shawarar da su kamar yadda ya kamata a yi ba, domin tattauna abin da za a kara wa masu matakin albashi na 07 zuwa sama ba.

Daga nan ya yi kira ga dukkan mambobin kungiyar na jiha baki daya da su kwantar da hankalin su, domin kungiyar su ta kwadago na nan na kokarin ganin tabbatacin sun kwato wa dukkan ma’aikatan jihar hakkokin su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel