Zaben Osun: Mawaki Davido Ya Shirya Kai Korafi ga Donald Trump na Amurka

Zaben Osun: Mawaki Davido Ya Shirya Kai Korafi ga Donald Trump na Amurka

  • Fitaccen mawakin Afrobeats, Davido, ya ce zai tuntubi Shugaban Amurka Donald Trump game da zaben gwamnan Osun
  • Davido ya bayyana cewa zai shiga siyasa ne kawai idan aka gudanar da zabe cikin gaskiya, adalci da kuma cikakken gaskiya ba tare da magudi ba
  • Mawakin ya ce yana sanya ido kan zaben Osun, yana mai gargadin wadanda ke da hannu za su dandana kudarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Osogbo, Osun - Fitaccen mawakin Afrobeats, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya yi gargadi game da zaɓen gwamnan Osun.

Davido ya ce zai nemi taimakon Shugaban Amurka Donald Trump idan ya ga an yi magudi a zaben gwamnan Osun mai zuwa.

Davido zai kai korafi ga Trump kan zaben Osun
Mawaki Davido da kawunsa, Gwamna Ademola Adeleke na Osun. Hoto: Davido.
Source: Twitter

Mawakin da ya lashe lambobin yabo ya bayyana hakan ne yayin wani shiri kai tsaye da ɗan wasan barkwanci wanda Yaje Guardian ta bibiya.

Kara karanta wannan

2027: Babban jigon APC a Arewa ya tada rigima, ya ce ba zai sake tallata Tinubu ba

Davido ya magantu kan neman kujerar takara

A cewar Davido, yana da farin jini da goyon bayan jama'a da zai iya taimaka masa ya yi nasara a siyasa.

Mawakin ya ce amma zai yi tunanin neman mukamin zabe ne kawai idan an gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci.

Ya ce:

“Har sai an samu gaskiya da sahihanci, sannan zan iya ci gaba da harkokin siyasa, domin babu wanda zai iya kayar da ni a kowane zaɓe. Idan aka gudanar da zaɓe cikin ’yanci da adalci, kowa ya fito ya jefa ƙuri’arsa, zan yi nasara. Amma saboda yadda tsarin yake, babu gaskiya da sahihanci; suna rubuta sakamakon zaɓe.”

Barazanar da Davido ya yi kan zaɓen Osun

Da yake magana kan zaben gwamnan Osun mai zuwa, mawakin ya ce yana sanya ido sosai kan abubuwan da ke faruwa, yana jiran ganin yadda tsarin zaben zai kasance.

Davido ya kuma ce idan bai gamsu da yadda aka gudanar da zaben ba, zai kai kukansa ga Shugaban Amurka Donald Trump da wasu manyan mutane masu tasiri, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

'Kuri'u 16 ka samu': Davido da Bashir Ahmad sun kaure da faɗa, sun ƙunyata juna

Ya kara da cewa:

"Ina son na gani me za su yi a zaɓen Osun, ina jiransu mu ga me za su yi.
“Zan yi wa Trump magana, zan kira Trump, kowa da kowa. Idan har yanzu ba su ga abin da ke faruwa ba, zan je gaban Fadar White House in ce, ‘Ku taimake mu.’ Suna ganin abin wasa ne.
“Trump zai ce kawai, ina ganin wani mawakin Najeriya ne yake turo min da saƙo. Kada ku damu, saƙona zai isa gare shi.’”

A karshen jawabinsa, Davido ya yi kira kai tsaye ga wadanda abin ya shafa kan zaben jihar Osun, wadda kuma ita ce jiharsa ta asali.

Davido ya yi shagube ga gwamnan APC

Mun ba ku labarin cewa Mawaki David Adeleke wanda aka fi sani da Davido ya ci gaba da jawo maganganu yayin da ake shirin zaben Osun.

Davido ya mayar wa Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, martani bayan ya soki Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, kan salon mulkinsa.

Okpebholo ya yi ikirarin cewa Adeleke ya fi mayar da hankali kan rawa maimakon gudanar da harkokin gwamnati yayin gangamin APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.