Samson Siasia ya nemi a kawo masa dauki kan mahaifiyarsa da masu garkuwa suka sace

Samson Siasia ya nemi a kawo masa dauki kan mahaifiyarsa da masu garkuwa suka sace

Tsohon dan wasa kuma tsohon kocin tawagar kwallon kafan Najeriya ta Super Eagles, Samson Siasia, ya ce kawo wa yanzu yana cikin mafi tsananin duhu na rashin sanin inda mahaifiyarsa ta ke wadda masu garkuwa da mutane suka sace watanni kadan da suka gabata.

Makonni goma da suka gabata ne Mrs Ogere Siasia mai shekaru 76 tare da wasu mutanen biyu, sun afka tarkon masu garkuwa da mutane a kauyen Odoni dake jihar Bayelsa kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

A yayin zantawa da manema labarai na jaridar BBC reshen wasanni, tsohon kocin na Najeriya ya ce ya zuwa yanzu, sawun wadanda suka yi garkuwa da mahaifiyarsa ya bace wa jami'an 'yan sanda ta yadda sun gaza sanin makamar da za su rika wajen gano inda take.

Siasia ya ce babban abin da ya fi damunsa a halin yanzu shi ne, matsananciyar rashin lafiya da mahaifiyar tasa ta kasance tana fama da ita tun gabanin masu garkuwa da mutanen suka yi awon gaba da ita.

Ya ke cewa yana cikin mafi kololuwar bakin ciki gami da zulumi a sanadiyar yadda babu dare babu rana tunani halin da mahaifiyarsa ke ciki a hannun masu ta'adar ta garkuwa, inda ya ke rokon da su sako masa ita ko ya samu sukuni.

KARANTA KUMA: PDP za ta tuntunbi shawarar Saraki, Jonathan, Wike da sauransu kan zaben 2023

A watan Agustan da ya gabata hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA, ta sanar da hukuncinta na dakatar da Siasia daga dukkanin wasu harkokin kwallon kafa har abada bayan ta kama shi da laifin rashawa wajen karbar na goro domin sauya sakamakon wasanni.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel