Abin Boye Ya Fito: Trump Ya Fadi Wanda Ya ke So Ya Gaje Shi a Amurka
- Shugaban Amurka Donald Trump ya shaida wa masu ba shi gudunmawar yakin neman zabe cewa yana son Mataimakin Shugaban Kasa JD Vance ya gaje shi a zaben 2028
- Trump ya fadi hakan ne yayin wata tattaunawar sirri da aka yi a Offis din Oval makonni biyu da suka gabata, a cewar wasu rahotanni da aka samu ta bayan fage
- Ko da yake ana kallon Ministan Taron Kasar, Marco Rubio a matsayin babban abokin hamayyar Vance, wasu masu masana sun yi gargadi cewa Trump na iya sauya ra'ayinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Washington – Shugaba Donald Trump ya fara fito da ra'ayinsa na gudanar da mulki bayan wa'adinsa, inda ya bayyana wa masu ba shi gudunmawa cewa yana son mataimakinsa, JD Vance ya zama dan takarar shugaban kasa a zaben 2028.
Wani rahoto ya nuna cewa Trump ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta sirri da ya yi da masu tura masa kudi a ofishinsa na Oval makonni biyu da suka gabata.

Source: Getty Images
Jerussalem Post ta ambato majiyoyi guda biyu da suka nemi a sakaya sunayensu suna cewa Trump ya shaida wa 'yan kasuwar cewa "A karshen komai, muna bukatar mu zabi JD."
Tsari da matsayin 'yan takara
Wani mai ba shugaban kasa shawara ya shaida cewa Trump ya riga ya yanke shawarar cewa Vance ne zai zama dan takarar jam'iyyar Republican.
A daya bangaren kuma, wasu masu ba shugaban shawara sun gargadi cewa Trump na iya sauya ra'ayinsa, domin yana fada wa mutane daban-daban abubuwa mabambanta.
Rahoton Yahoo News ya nuna cewa wani jami'i ya ce:
"Duk wanda yake tunanin wannan abu ne da aka riga aka gama shi, yana sauri ne kawai, ko kuma ba ya kusa da shugaban kasar sosai."
Hamayya tsakanin Vance da Rubio
Ana kallon Marco Rubio a matsayin babban abokin hamayyar Vance a zaben shekarar 2028, wanda ke samun karbuwa sosai a tsakanin Amurkawa da Yahudawa.

Kara karanta wannan
2027: Babban jigon APC a Arewa ya tada rigima, ya ce ba zai sake tallata Tinubu ba
Shi dai Vance har yanzu bai sanar da matayarsa ba, inda wani na kusa da shi ya bayyana cewa yana jiran wasu abubuwa ne kafin ya yanke shawara.

Source: Getty Images
Wani masani ya kara da cewa Trump zai so ya ga Rubio da Vance a tikiti guda na haɗin gwiwa, amma har yanzu ba a san ko Rubio zai yarda ya kasance mataimakin Vance ba.
Gargaɗin Vance kan El-Sayed
A wani labarin, mun ruwaito cewa Mataimakin Shugaban Kasa JD Vance ya dauki hankalin jama'a bayan da ya yi amfani da kalmar ba'a ga Abdul El-Sayed a matsayin "Shugaba Abdul El-Sayed."
Wannan furuci na Vance ya zo ne kwanaki kadan bayan da El-Sayed ya samu nasara a zaben fitar da gwani na jam'iyyar Democrat kan 'yar majalisa Haley Stevens a zaben majalisar dattawa ta jihar Michigan.
Yayin da yake magana a wani taro na yaki da ha'inci tare da mataimakin shugaban ma'aikatan White House Stephen Miller, Vance ya yi gargadi kan yiwuwar samun gwamnatin El-Sayed a nan gaba.
Asali: Legit.ng
