Ana tsakiyar Yakin Iran, Cutar da Ta Kama Tsohon Shugaban Kasar Amurka Ta Kara Tsanani

Ana tsakiyar Yakin Iran, Cutar da Ta Kama Tsohon Shugaban Kasar Amurka Ta Kara Tsanani

  • Dan tsohon shugaban kasar Amurka, Hunter Biden ya ce ciwon dajin mahaifinsa, Joe Biden, ya bazu zuwa ƙasusuwansa kuma yana ci masa rai
  • Ya bayyana cewa ciwon yana da tsanani kuma yana raunana tsohon shugaban Amurkan sosai a halin yanzu
  • Joe Biden ya bayyana a watan Mayun 2025 cewa an gano yana da wani nau'in ciwon daji mai tsanani na prostate

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

United States - Hunter Biden, ɗan tsohon shugaban Amurka Joe Biden, ya bayyana cewa ciwon dajin da mahaifinsa ke fama da shi ya kara tsananta matuka.

Ya ce cutar dajin ta bazu zuwa ƙasusuwansa, yana mai cewa yanayin lafiyarsa ya zama abin damuwa ga iyalinsu.

Biden.
Tsohon shugaban kasar Amurka, Joe Biden lokacin yana kan mulki Hoto: Samuel Corum
Source: Getty Images

Hunter ya bayyana hakan ne a wata hira da BBC da aka wallafa ranar Asabar, yayin da yake magana kan yadda mahaifinsa ke fama da cutar daji.

Kara karanta wannan

Wuta ta yi wuta: Babban sojan Amurka na neman a fita a yaki da Iran

Halin da tsohon shugaban Amurka ke ciki

Ya ce cutar ta bazu zuwa ƙasusuwan Joe Biden kuma tana haifar masa da matsanancin ciwo da raunana jikinsa.

“Ina fatan zai fi yin korafi, saboda lamarin ba shi da kyau. Ciwon dajin ya bazu. Yana da matukar ciwo kuma yana raunana shi sosai. Ciwon daji abu ne mai matukar wahala. Abin bakin ciki ne kallon yadda yake fama da shi,” in ji shi.

Hunter, wanda shi ne ɗa guda tilo na Joe Biden da ke raye, ya kuma bayyana irin muhimmancin da mahaifinsa ke da shi a cikin iyalinsu.

“Mahaifina har zuwa yau shi ne ginshikin iyalinmu. Shi ne uba mafi kyau, miji mafi kyau da kuma kaka mafi kyau,” in ji Hunter.

Yaushe aka gano ciwon Biden?

Joe Biden ya sanar a watan Mayun 2025, watanni huɗu bayan barin fadar White House, cewa an gano yana fama da wani nau'in ciwon daji mai tsanani na prostate.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fadi yadda ake kashe tulin bashi da ake laftowa Najeriya

Bayan gano cutar, tsohon shugaban Amurkan ya bayyana cewa maganinsa na tafiya yadda ya kamata, tare da nuna godiya ga mutanen da suka ci gaba da yi masa addu'a da fatan samun sauƙi.

A watan Yulin 2026, Biden ya ce yana karɓar magani kuma yana ganin ci gaba mai kyau.

Biden ya taba nuna kwarin gwiwa

A farkon lokacin da aka gano cutar, Biden ya yi magana cikin kyakkyawan fata game da yiwuwar maganinsa, yana mai cewa likitocinsa sun yi imanin cewa zai amfana daga maganin da ake ba shi.

Ya ce:

“Hasashen yana da kyau, muna aiki a kai. Abin ya ta'allaka ne kan shan wani magani na musamman na tsawon makonni shida. Kuma ana sa ran za mu iya shawo kan cutar.”

Sai dai sabbin kalaman Hunter sun nuna cewa cutar na ci gaba da zama babban kalubale ga Biden da iyalinsa, cewar rahoton Punch.

Bide.
Tsohon shugaban kasar Amurka, Joe Biden a wurin taro Hoto: Samuel Cirum
Source: Getty Images

Amurka na kokarin sulhu da Iran

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa yana kokarin ganin an kawo karshen yaki da Iran nan ba da jimawa ba.

Kara karanta wannan

Abin boye ya fito: Trump ya fadi wanda ya ke so ya gaje shi a Amurka

Shugaba Trump ya yi wannan bayani ne yayin da yake amsa tambayoyin 'yan jarida game da farashin makamashi a Amurka da kuma kasuwannin duniya.

Trump ya kuma ƙaryata rahotannin da ke cewa Amurka na fuskantar ƙarancin makamai, yana mai cewa hakan ba gaskiya ba ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262