Wata uwa a Najeriya ta fadi dalilin da yasa ta amince dan cikinta ya yi mata ciki

Wata uwa a Najeriya ta fadi dalilin da yasa ta amince dan cikinta ya yi mata ciki

Wata uwa, uwargida Veronica Iorshe, mai shekaru 47, da ke zaune a garin Ugee, karamar hukumar Gwer, a jihar Benuwe, ta bayyana yadda ta dinga kwanciya da dan cikinta har ta kai ya yi mata ciki.

A cewar Veronica, "ni ba lalatacciyar mace ba ce. Ni mace ce dake son mijinta saboda bana son rabuwa da shi.

"Na aikata hakan ne don na kubutar da aure na, amma na kan ji nauyin abin da na aikata wasu lokutan. Na san da nauyi, amma da gaske ne na kwanta da dan cikina. Na yi hakan ne don na haifa wa mijina da. Amma sabanin yin hakan ya kubutar da aurena, sai gashi ya lalata shi."

Veronica ta ce ta yanke shawarar fara kwanciya da dan cikinta mai shekaru 20 bayan ta shafe shekaru takwas ba tare da samun haihuwa tare da sabon mijinta ba. Ta bayyana cewa batun rashin samun haihuwar yasa surukarta ta fara tsangwamarta.

"Na kula cewa ba yarinya nake koma wa ba, kuma gashi mahaifiyar mijina ta fara tsangwamata tana cewa ina cin kudin dan ta ba tare da haifa masa komai ba. Daga baya ta zo ta fara zargin cewa na girme shi, ina yi masa wayo.

"Lamarin ya yi tsananin da daga karshe sai da surukata ta kori da na daga gidan tare da fadin cewa danta ba zai cigaba da ciyar da mu a banza ba, hakan yasa sai garin Lafiya na je na kama masa hayar shago," a cewar Veronica.

DUBA WANNAN: An kama kurtun soja da kananan buhunhunan tabar wiwi 169 a Jigawa

Veronica ta ce duk kokarin bawa mijinta shawara a kan su je gwaji ya ci tura, ita kuma bata son cin amanarsa da wani a waje.

"Ina son gwada kai na domin na sani ko nice keda matsala, kuma gashi ba zan iya cin amanar mijina ba. Hakan ne yasa na fara kusantar da na, Simon, tare da kwanciya da shi, musammam a lokatun da na san zan iya daukan ciki. Na san yin hakan ba abu ne me kyau ba, amma ya fi yi min sauki," a cewarta.

A nasa bangaren, mijin Veronica mai suna Sebastian ya ce bai ji dadin cin amanar da matarsa ta yi masa ba, tare da bayyana cewa ba zai taba yafe mata ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel