Masu garkuwa da mutane sun sace wata sabuwar amarya a hanyarta ta zuwa Sokoto

Masu garkuwa da mutane sun sace wata sabuwar amarya a hanyarta ta zuwa Sokoto

Rahotanni sun kawo cewa yan bindiga da ake zatton masu garkuwa da mutane ne sun sace wata Halimatu Abdullahi Bunun.

A cewar rahotannin, anyi garkuwa da Halima wacce ta kasance sabuwar amarya a hanyarta ta zuwa jihar Sokoto daga Kauran Namoda da ke jihar Zamfara.

Hakazalika wani mai amfani da shafin sadarwa ta Facebook, Hon Dayyabu Mande Tsafe ya wallafa labarin a shafinsa, inda ya rubuta “inna illahi wa inna alaihin raji un, masu garkuwa da mutane sunyi garkuwa da kaunata halimatu bunun bela allah yaimaki mafita.”

KU KARANTA KUMA: Muna amfani da inifam dinmu wajen fashi a manyan tituna – Korarrun sojoji

A wani labari makamancin haka Legit.ng ta rahoto a baya cewa masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da mataimakin shugaban karamar hukumar Charanchi na jihar Katsina, Aminu Hassan.

Wasu mutane da ba a san ko su wanene ba suka sace Hassan daga kauyensu, 'Yan Albasa a daren ranar Talata. Wasu na kusa da iyalansa sun ce Hassan na tare da iyalansa lokacin da mutanen suka dira gidansa suka yi awon gaba da shi.

Kakakin 'yan sandan jihar, SP Isha Gambo ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce 'yan sanda sun bazama cikin daji da niyyar ceto shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel