An Yi Babban Rashi: Mahaifin Fitaccen Dan Kwallon Duniya, Lionel Messi Ya Mutu

An Yi Babban Rashi: Mahaifin Fitaccen Dan Kwallon Duniya, Lionel Messi Ya Mutu

  • Mahaifin kyaftin ɗin Argentina kuma shahararren dan wasan kwallo, ionel Messi, Jorge Messi, ya rasu yana da shekaru 68 a duniya
  • Jorge ya rasu ne da misalin ƙarfe 10:00 na dare ranar Juma’a a wani asibitin musamman da ke Rosario, Argentina, bayan fama da doguwar rashin lafiya
  • Ya taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa Lionel Messi ya fara samun kulawar lafiya da kuma komawa Barcelona yana da shekaru 13

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza Daudawa ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Kasar Argentina - Mahaifin Lionel Messi, Jorge Messi, ya yi bankwana da duniya yana da shekaru 68 a duniya.

Jaridar MARCA ta ruwaito rasuwar mahaifin Messi a ranar Asabar, 8 ga watan Agustan 2026 tana ambaton kafar yaɗa labarai ta Argentina, Infobae.

Mahaifin Messi ya bar duniya
Lionel Messi na kuka bayan rashin nasarar Argentina Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Wani bincike mai zaman kansa da jaridar Punch ta gudanar kan rahoton Infobae da wasu kafafen yaɗa labarai ya tabbatar da cewa Jorge ya rasu da misalin ƙarfe 10:00 na dare ranar Juma’a, 7 ga watan Agustan 2026.

Kara karanta wannan

Wuta ta yi wuta: Babban sojan Amurka na neman a fita a yaki da Iran

A ina mahaifin Messi ya mutu?

Jorge Messi ya mutu ne a wani asibitin musamman da ke Rosario, Argentina, bayan fama da doguwar rashin lafiya.

Mahaifin na shahararren dan wasan wanda ya yi aure da Celia Cuccittini, yana da ’ya’ya huɗu, Lionel, Rodrigo, Matias da Maria Sol.

Ya taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa ɗansa, Lionel, tun yana matashin ɗan wasa a Newell’s Old Boys har zuwa lokacin da ya zama ɗaya daga cikin fitattun taurarin ƙwallon ƙafa a duniya.

Musamman, Jorge ya taka rawa wajen ganin Lionel ya samu maganin da yake buƙata bayan an gano cewa matashin yana buƙatar maganin sinadarin hormone na haɓaka jiki.

Ya taimaki Messi zuwa Barcelona

Bayan ƙoƙarin ganin an samu maganin a Argentina ya ci tura, Jorge ya taimaka wajen shirya tafiyar ɗansa zuwa Barcelona yana da shekaru 13.

Daga bisani, ya zauna tare da Lionel a Spain a farkon shekarun da ɗan nasa ke fuskantar ƙalubale wajen fara rayuwar ƙwallon ƙafa a Turai, yayin da sauran ’yan uwansu suka ci gaba da zama a Rosario.

Kara karanta wannan

Diomande, Osimhen: Jerin 'yan wasan Afrika 10 mafi tsada a tarihin kwallon kafa

A wata hira da aka yi da shi a shekarar 2007, Lionel ya tuna cewa mahaifinsa ya tambaye shi ko yana son ci gaba da bin burinsa a Spain ko kuma ya koma gida.

“Babana ya kasance tare da ni a kowane lokaci. Mun fuskanci lokuta masu wahala da dama,” in ji Messi.

Ya ƙara da cewa:

“Babana ya tambaye ni, me kake son yi, kana son mu ci gaba ne ko kuma mu koma? Ina son ci gaba, sai ya zauna tare da ni.”
Mahaifin Messi ya mutu
Jorge Messi a wajen kallon wasan Argentina Hoto: Jean Catuffe
Source: Getty Images

Wannan shawara ta zama ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da suka sauya rayuwar Messi a ƙwallon ƙafa, yayin da ya ci gaba da kafa tarihi a Barcelona, daga bisani ya zama ɗaya daga cikin ’yan wasan da suka fi samun nasarori a tarihin ƙwallon ƙafa.

Jorge ya kuma zama muhimmin mutum wajen kula da harkokin ɗansa a wajen fili, ciki har da tattaunawa da manyan kamfanoni da shahararrun kamfanoni na duniya.

Abin da Messi ya ce kan rashin nasarar Argentina

A wani labarin kuma, kun ji cewa Lionel Messi ya yi magana bayan tawagarsa ta sha kashi a hannun Spain a wasan karshe na gasar cin kofin duniya ta FIFA 2026 a Amurka.

Dan wasan gaba na Inter Miami FC ya amince cewa zai yi wuya a shawo kan wannan rashin nasara, amma ya bayyana alfahari da irin nasarar da tawagarsa ta samu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com