Barin zance: Yadda hadimin Ganduje ya ‘kaskantar’ da mataimakin shugaban kasa Osinbajo

Barin zance: Yadda hadimin Ganduje ya ‘kaskantar’ da mataimakin shugaban kasa Osinbajo

Guda daga cikin hadiman gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ta bangaren watsa labaru, Salihu Tanko Yakasai ya kira ruwa da wata kasassaba daya tafka a shafin kafar sadarwar zamani ta Twitter, inda ya yi ma mataimakin shugaban kasa Osinbajo shagube.

Jaridar Punch ta ruwaito Yakasai ya bayyana mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne a matsayin ‘Mataimakin shugaban kasa mai kula da al’amarin karatu’ ta shafinsa mai adireshi @dawisu.

KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane sun halaka babban jami’in Dansanda a hanyar Kogi-Abuja

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Yakasai ya fadi haka ne yayin da yake mayar da martani ga batun da wani ma’abocin Twitter mai suna Ismail Kabir ya yi, inda yake cewa “Da alama duk wani mai fada a ji a Najeriya ya tafi New York domin halartar taron majalisar dinkin duniya.”

Manufar Kabir shi ne shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da manya manyan jami’an gwamnatin Najeriya sun tafi Amurka domin halartar taron majalisar dinkin duniya, amma sai Yakasai ya yi caraf, ya ara ya yafa da cewa: “Mataimakin shugaban kasa mai kula da al’amarin ilimi na nan”

Wannan barin zance na Yakasai ya janyo cece kuce tare da tayar da kura musamman duba da batun da ake watsawa a kafafen sadarwa na cewa manyan hadiman shugaba Buhari na kokarin karya lagon Osinbajo tare da rage masa karsashi kafin zaben 2023.

Sai dai bayan samun zafafan raddi daga wajen ma’abota kafar sadarwa ta Twitter sai Yakasai ya bayyana kansa a matsayin babban masoyin Osinbajo, amma duk da haka aikin gama y agama, magana kuma zarar bunu ce, sakamakon hakan sai ya kara tayar da kura.

Wani mai suna @dsalahu yace: “Maigida, babban masoyin mataimakin shugaban kasa ba zai yi raha da shi ba a matsayin ‘mataimakin shugaban sa na bangaren ilimi’ musamman a wannan lokaci ba, fitowar maganar daga bakin hadimin gwamna ya fi muni.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel