Allah Sarki: An kama wani karamin yaro Musulmi dan shekara 4 saboda ya jefi motar 'yan sanda a kasar Isra'ila

Allah Sarki: An kama wani karamin yaro Musulmi dan shekara 4 saboda ya jefi motar 'yan sanda a kasar Isra'ila

- Jami'an 'yan sanda sun je har gida sun kama wani yaro dan shekara hudu a duniya a garin Palastine

- 'Yan sandan wadanda suke na kasar Isra'ila ne sun zargi cewa yaron ya jefi motarsu ne a lokacin da suke wucewa

- Yaron mai suna Muhammad Rabi Elayyan wanda yake Musulmi ne, mahaifinsa ya karyata wannan zargi

Kasar Isra'il ta kira wani yaro dan karamin yaro dan shekara hudu Musulmi dan kasar Palastine daga yankin Gabashin Jarusalam, domin binciken shi.

Yaron mai suna Muhammad Rabi Elayyan wasu jami'an 'yan sanda ne masu yawan gaske suka je har gida suka wuce dashi zuwa ofishin 'yan sanda dake Salah Eddin Street, kusa da tsohon birnin Damascus.

Bayan wannan kira da 'yan sandan suka yiwa Elayyan, mahaifinshi ya dauke shi da kanshi ya kai shi ofishin 'yan sandan, inda aka nuno wani bidiyo na yadda mutane ke kuka lokacin da aka wuce da yaron ofishin 'yan sandan, inda suke bashi kwarin guiwa cewa kada yaji tsoro.

'Yan sandan kasar Isra'il din sun yi zargin cewa Muhammad yana jifan motocinsu, hakan ya saka suke son binciken shi. Sai dai kuma mahaifin yaron ya karyata wannan zargi da 'yan sandan suke yi, inda yace dan shi yana wasa da yara ne 'yan uwansa a lokacin da suka yi wannan zargin.

KU KARANTA: Wani gari da ake biyan zauna gari banza naira dubu talatin (N30,000) a kowacce rana su dinga kwashe shara

Mahaifin yaron mai suna Rabi ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Palestine inda ya ce: "Yau da safe nake gayawa dana Muhammad cewa zan kai shi wajen wanka, ban san mai ya faru ba, amma munyi mamaki da muka ga sojoji sun cika kofar gidanmu."

A lokacin da mahaifin yaron ya isa ofishin 'yan sandan da dan shin, 'yan sandan sun hana Muhammad shiga ofishin nasu, inda suka shiga da mahaifinsa suka fara yi masa tambayoyi.

'Yan sandan sun bayyanawa mahaifin yaron cewa idan har bai hana yaron jifan su ba zasu raba shi da danshi gaba daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel