Sheikh Pantami yayi bayani akan sabuwar gaisuwar zamani da ya kirkira da mata

Sheikh Pantami yayi bayani akan sabuwar gaisuwar zamani da ya kirkira da mata

Babban malamin nan na addinin Musulunci kuma ministan sadarwa, Sheikh Isa Pantami yayi jawabi akan sabon sigar gaisawa da mata ba tare da an hada hannu ba wacce yayi wa lakabi da “wireless greetings”.

A cewar malamin hakan sabuwar fasaha ce wacce ke ba mutum damar gaisawa ba tare da cudanya ba sannan kuma an kiyaye dokokin Allah a ciki.

A wata hira da yayi da shafin BBC Hausa, Pantami yace: “An shigo da sabuwar gaisuwa ta zamani da mata, idan ka girgiza hannunka fasaha ce. Mu mutanen ICT aikinmu yana da alaka da zuwa da sabbin na’urori da kuma kimiyya da fasaha da kuma tsarin abubuwa.

“Da idan za ka shiga intanet sai an kawo waya an hada da komfuta. Amma yanzu akan wayarka babu waya saboda akwai intanet, saboda haka wannan gaisuwa da mata wireless ne kamar Intanet, ba sai ansa waya ba.

KU KARANTA KUMA: Yan majalisar dokokin jihar Sokoto na APC 2 sun lallasa yan PDP a kotun zabe

“Ka ga na farko gaisuwar wireless, kwararru kan fasahar sadarwa sun yi aikinsu. To shine sai mu karkada hannu wireless, ba sai an hada ba, in aka kada anyi wireless, kuma sannan an kiyaye dokokin Allah a ciki."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel