Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'adda, an Kashe fiye da 65 yayin da Aka Ceto Mutane 360

Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'adda, an Kashe fiye da 65 yayin da Aka Ceto Mutane 360

  • Sojojin Najeriya sun hallaka ’yan ta’adda 69 tare da cafke wasu 49 da ake zargi da aikata laifuka a ayyukan mako guda
  • Dakarun sun ceto sama da mutane 360 da aka yi garkuwa da su a sassan Arewa da Neja Delta
  • Rundunar ta kuma tarwatsa matatun mai guda uku tare da kwato sama da lita 251,600 na danyen mai da ake zargin an sace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Abuja - Hedikwatar Tsaron Najeriya ta ce dakarun sojin kasar sun hallaka ’yan ta’adda 69, sun ceto sama da mutane 360 da aka yi garkuwa da su tare da cafke wasu 49 da ake zargi da aikata laifuka cikin mako guda.

Daraktan Ayyukan Yada Labarai na Tsaro, Manjo Janar Michael Onoja, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai kan ayyukan da sojoji suka gudanar a sassan kasar.

Kara karanta wannan

Sojoji sun shafe mako suna ruwan wuta kan 'yan ta'adda, an kashe 69

Dakarun Hadin Kai sun ceto mutane

Sai dai ya ce wani soja ya rasa ransa yayin gudanar da ayyukan, yayin da wani kuma ya samu raunuka, kamar yadda rahoton Vanguard ya nuna.

A Arewa maso Gabas, dakarun Operation Hadin Kai sun dakile yunkurin ’yan ta’adda na yin garkuwa da fararen hula a hanyar Buratai-Kamuya da ke karamar hukumar Biu a Jihar Borno.

Sojojin sun bi sawun ’yan ta’addan zuwa Mangari-Dora, inda suka ceto mutane 31 da suka hada da maza 22, mata biyar da yara hudu. An kuma kwato motoci hudu da babur daya.

A kusa da gadar Amuda a Gwoza, sojojin sun sake ceto mata biyu da yara biyu da aka tsare tun lokacin noman shekarar 2023.

Haka kuma, wasu ’yan uwa na mutanen da ake zargi da kasancewa ’yan ta’adda sun mika wuya a Gwoza, Konduga da Bama, yayin da wasu 20 suka mika wuya a Kwuari.

Kara karanta wannan

Tsugune ba ta kare ba, an rena kokarin Tinubu kan ceto daruruwan mutane da aka sace

An ceto mutane 308 a Neja

Daya daga cikin manyan nasarorin da aka samu shi ne ceto mutane 308 da aka yi garkuwa da su a Kainji Lake National Park da ke karamar hukumar Borgu ta Jihar Neja.

DHQ ta ce 163 daga cikin wadanda aka ceto sun fito ne daga kauyen Woro na Jihar Kwara, yayin da 145 suka fito daga Jihar Neja.

A Kogi kuma, sojoji sun dakile wasu yunkurin garkuwa da mutane tare da ceto mutane biyu da kuma hallaka wani dan ta’adda. Sai dai wani jami’in tsaron sa-kai ya rasa ransa.

An kwato danyen mai

A yankin Neja Delta, dakarun Operation Delta Safe sun ceto mutane 11 da aka yi garkuwa da su a hanyar Legas-Benin ta Jihar Edo.

Rundunar ta kuma tarwatsa matatun mai guda uku ba bisa ka’ida ba a Ogba-Egbema-Ndoni na Jihar Rivers, inda ta kwato lita 61,000 na kayayyakin man fetur, ciki har da lita 43,000 na danyen mai da ake zargin an sace.

Kara karanta wannan

Yadda za ku duba sunayen waɗanda hukumar Kwastam ta ɗauka aiki a 2026

A ranar 5 ga Agusta, an sake kwato lita 85,300 na kayayyakin danyen mai, yayin da ranar 6 ga Agusta aka gano lita 105,000 a Oteghele na Jihar Delta.

An kama masu safarar makamai

A yankin Arewa ta Tsakiya, Operation Whirl Stroke ta cafke Victor Idoko da ake zargi da safarar makamai a Makurdi, Jihar Benue, inda aka kwato bindigogi kirar gida guda biyu.

Sojojin sun kuma ceto mutane bakwai da aka yi garkuwa da su a hanyar Wukari-Zaki-Biam tare da mayar da su ga iyalansu.

A Nasarawa kuwa, an cafke mata biyu tare da kwato mujallun harsasai na AK-47 guda 10 dauke da harsasai 551.

Oluyede ya yabawa sojoji

A Kudu maso Gabas, dakarun Operation Udoka sun cafke wasu da ake zargi da hannu a wani kwanton bauna da aka kai wa sojoji a baya.

A Enugu, an cafke wasu mutum biyar da ake zargi mambobin IPOB ne, tare da kwato bindigogin General Purpose Machine Gun guda biyu da sauran makamai.

Babban Hafsan Hafsoshin Tsaro, Janar Olufemi Oluyede, ya yabawa dakarun bisa jajircewa da sadaukarwar da suke yi wajen kare kasa.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Mutanen gari sun sassara wata mata da adda har ta mutu a Bauchi

Ya kuma bukaci jama’a su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai domin taimakawa wajen dakile ayyukan ’yan ta’adda, masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka.

Ya tabbatar da cewa sojoji za su ci gaba da gudanar da ayyukansu har sai an dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com