Abubuwa 10 da ya kamata ku sa ni game da cutar shawara
A cikin ‘yan watanni da suka shude cutar shawara ta kashe sama da mutane 40 kamar yadda rahotanni suka bayyana mana a kasar nan wato Najeriya.
Sauro ne yake dauke da kwayar cutan shawara kuma ana kamuwa da ita ta hanyar cizon sauron. Haka zalika cutar shawara , ana iya maganceta ta hanyar rigakafi kuma tana yaduwa ne ta hanyar cizon sauron kadai.
KU KARANTA:An tafka muhawara a Majalisar wakilan Najeriya game da kananan hukumomin da ‘yan Boko Haram suka mamaye
Ga jerin wasu ababe 10 da ya kamata ku sa ni game da wannan cuta ta shawara:
1. Rigakafi ita ce hanya mafi da cewa wurin maganin wannan cuta mai kisan mutane.
2. Ana iya magance cutar idan aka dau mataki a kanta kafin ta bunkasa a jiki dan –adam.
3. Alamun cutar na bayyana ne cikin kwana shida, wadannan alamun sun hada da, masassara, ciwon kai da ciwon baya.
4. Kimanin 15% cikin masu cutar ta kan zarce zuwa rashin lafiya mai tsanani wadda kan iya haifar da zuban jini, rashin aikin wasu gabobin jiki da kuma mutuwa.
5. Rigakafin kan iya zama illa ga mutanen da suka haura shekara 60 da haihuwa.
6. Haka ma mace mai ciki, rigakagin kan iya zama illa gareta, an so ta tuntubi likata kafin tayi rigakafin.
7. Idan har rigakafin ba ta samu ba, ana iya amfani da maganin sauro iri daban-daban.
8. Dolene sai mutum yayi rigakafi idan zai tafi daya daga cikin kasashen Kudancin Amurka.
9. Ga masu tafiya kuwa kasashen da ke fama da cutar shawaran ana so mutum yayi allurar rigakafi a cikin kwanaki goma da shigarsa kasar.
10. 10.99% na wadanda suka yi allurar rigakafin na damar cin karfin kwayar cutan cikin wata guda da kuma har illa masha Allahu.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng