An Ji Dalilin Saudiyya da Ta Garkame Wasu 'Yan Najeriya a Gidan Yari
- Jakadan Najeriya a Saudiyya ya ce wasu ’yan Najeriya na ci gaba da zama a gidan yari duk da sun kammala zaman hukunci da aka yanke masu
- Ofishin Jakadancin Najeriya ya umarci dukkan ƙungiyoyin ’yan 'kasar da ke Saudiyya su haɗa kai ƙarƙashin inuwa ɗaya domin sauƙaƙa hulɗa da warware matsalolinsu
- Shugabar NiDCOM, Abike Dabiri-Erewa, ta ce lokaci ya yi da za a fara nuna nasarorin ’yan Najeriya da ke Saudiyya, ba wai a riƙa jin labaran masu laifi kaɗai ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Jakadan Najeriya a ƙasar Saudiyya, Dakta Yakubu Gambo, ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu ’yan Najeriya ke ci gaba da zama a gidajen yari da cibiyoyin tsare mutane a ƙasar.
Ya ce mutanen wanda yan asalin kasar nan ne na ci gaba da zaman ne duk da sun kammala zaman hukuncinsu, saboda sun kasa biyan tarar da aka ci su.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Gambo ya bayyana hakan ne ranar Alhamis 7 ga watan Yuli, 2026 yayin da ya kai wa Shugabar Hukumar ’Yan Najeriya Mazauna Ƙasashen Waje (NiDCOM), Abike Dabiri-Erewa, ziyara a hedikwatar Abuja.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Jami’ar Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a da Tsare-tsare ta NiDCOM, Violet Nwosu, ta sanya wa hannu.
An tsare yan Najeriya a Saudiyya
Jaridar Vanguard ta ruwaito jakadan ya ce jin daɗin ’yan Najeriya da ke zaune a ƙasashen waje na daga cikin abubuwan da ya bai wa fifiko tun bayan hawansa mulki.
Ya kuma ce Ofishin Jakadancin Najeriya ya umarci ƙungiyoyin ’yan Najeriya da ke Saudiyya su haɗa kansu ƙarƙashin inuwa ɗaya domin ƙarfafa haɗin kai da kuma sauƙaƙa wa ofishin jakadancin tattaunawa da su kan matsalolin da suka shafe su.

Source: Facebook
Ya ce:
“Ofishin jakadanci ya umarci ƙungiyoyin ’yan Najeriya daban-daban su haɗa kansu ƙarƙashin inuwa ɗaya domin ƙarfafa haɗin kai da kuma bai wa ofishin jakadanci damar yin hulɗa mai ma’ana da inganci wajen magance duk wata matsalar da ta shafi ’yan Najeriya mazauna ƙasashen waje.”

Kara karanta wannan
Atiku da Peter Obi sun tafka kuskure, an cire su daga barazanar da Tinubu zai fuskanta a 2027
Yan Najeriya na fuskantar kalubalae
Sai dai Gambo ya ce har yanzu suna fuskantar ƙalubale da suka shafi wasu ’yan Najeriya da ke tsare a gidajen yari da ke sassan Saudiyya.
A kalamansa:
“Muna kuma fuskantar ƙalubalen da suka shafi ’yan Najeriya da ke gidajen yari da cibiyoyin tsare mutane, ciki har da waɗanda suka kammala zaman hukuncinsu amma ba za su iya komawa gida ba saboda tarar da har yanzu ba su biya ba.”
Jakadan ya ce ba daidai ba ne a ɗauka cewa mafi yawan ’yan Najeriya da ke Saudiyya suna da alaƙa da aikata laifi, domin akwai mutane da dama da suka yi fice a sana’o’i da kasuwanci.
Saudiyya ta hada kai da kasashen Musulmi
A baya, kun samu labarin cewa Yariman Saudi, Mohammed bin Salman, Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan, da Firayim Ministan Pakistan Shehbaz Sharif za su sanya hannu kan yarjejeniyar tsaro.
Majiyoyi sun bayyana cewa sauye-sauyen da ake samu ta fuskar tsaro da tashin hankali a yankin Gabas Tsakiya ne suka hanzarta cimma wannan kawance tsakaninsu wanda zai inganta tsaron yankin.
Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar Saudi Arabia ke fuskantar hare-haren jiragen sama marasa matuki da aka harbo daga yankin kasar Iraki kuma ana ci gaba da gwabza yaki da Iran.
Asali: Legit.ng
