Yanzu-yanzu: Osinbajo ya bukaci Google ta janye wani faifan bidiyonsa da aka wallafa a YouTube

Yanzu-yanzu: Osinbajo ya bukaci Google ta janye wani faifan bidiyonsa da aka wallafa a YouTube

Lauyoyin Femi Atoyebi & Co, a madadin mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo sun rubuta wasika ga kamfanin Google inda suke neman a janye wani bidiyo da shafin Roots TV ta wallafa a kafar YouTube.

A cewar wasikar da The Cable da gani, Roots TV ta wallafa wani bidiyo ne mai dauke da kararrayi da bata sunan Osinbajo.

"Mun fahimci cewa wata kafar yada labarai na intanet mai suna Roots TV ya wallafa wani bidiyo a wannan addreshin... mai dauke da abubuwan cin mutunci ta hanyar amfani da kafar ku."

"A cikin bidiyon da aka wallafa a shafin Roots TV Nigeria a ranar 20 ga watan Satumban 2019, an fadi wadanan kalaman da ba gaskiya bane:

DUBA WANNAN: An gina makaranta a kauyen Kano da babu mai wata shaidar kammala karatu

a. Wanda muke karewa yana kwashe kudin gwamnati da ke karkashinsa da zargin cewa yana amfani da hukumar tattara haraji na tarayya (FIRS) domin aikata zambar.

b. Wanda muke karewa ya gaza kare kansa kan tsaikon da aka samu a asusun FIRS yayin da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Mr Abba Kyari ya yi masa tambayoyi.

c. Wanda muke karewa ya gaza yin bayanin yadda aka rarraba kudin mutanen da ke amfana da shirin tallafin gwamnatin tarayya na NSIP a jihar Adamawa.

"Wanda muke karewa yana neman ku janye bidiyon nan take ko kuma dakatar da shafin na Roots TV a kafar YouTube."

Wasikar mai dauke da sa hannun Osaro Eghobamien da Femi Atoyebi ta ce mataimakin shugaban kasar zai shigar da kara kotu idan ba janye bidiyon ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel