An Dauki Gwamna 1 daga Arewacin Najeriya an ba Shi Lambar Yabo ta ZIK a Kasar Waje
- An karrama Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara da lambar yabo ta zaman lafiya da kyayyawan shugabanci a kasar Ghana
- An yabawa gwamnatinsa kan sauye-sauyen tattalin arziki da shugabanci nagari a Zamfara da ke Arewa maso Yamma
- Gwamnan ya ce lambar yabon za ta kara masa kwarin gwiwar yin aiki domin ceto jihar daga dukkan wani kalubale
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ghana - Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya samu lambar yabo ta ZIK International Peace and Leadership Award a kasar Ghana.
An karrama Gwamna Lawal da wannan lambar yabo ne saboda nasarorin da gwamnatinsa ta samu cikin shekaru uku da suka gabata.

Source: Facebook
Daily Trust ta ruwaito cewa an gudanar da bikin bayar da lambar yabon karo na 7 a ranar Juma’a, 7 ga watan Agusta, 2026 a British Council da ke Accra, babban birnin Ghana.
Kwamitin gudanarwa da majalisar kula da lambar yabon ZIK sun ce daga cikin dalilan karrama Gwamna Dauda Lawal akwai gagarumin ci gaba da ya samu a fannin shugabanci da sauye-sauyen tattalin arziki a Jihar Zamfara.
An yabi salon shugabancin Dauda Lawal
Shugaban kwamitin amintattu na ZIK Pan-African Award, Farfesa Echefuna R.G. Onyeabadi, ya bayyana cewa manufar lambar yabon ita ce karrama mutanen da ke bayar da gagarumar gudunmawa wajen yi wa al’umma hidima.
Bayan karbar lambar yabon, Gwamna Dauda Lawal ya nuna godiyarsa, tare da alkawarin kara kaimi wajen ceto da sake gina Jihar Zamfara.
Ya ce:
“Na sadaukar da wannan lambar yabo ga daukacin al’ummar Jihar Zamfara. Gwamnatina ta yi ta kokari tukuru domin tabbatar da cewa jihar za ta iya gogayya da kowace jiha a Najeriya.
"Wannan shi ne alkawarin da muka dauka, kuma cikin shekaru uku kacal mun zarce abin da ake tsammani.”
Gwamna ya bayyana nasarorin Zamfara
Gwamna Lawal ya ce gwamnatinsa ta sauya fasalin Zamfara ta hanyar ayyukan sabunta birane, tare da gina filin jirgin sama na zamani wanda ba a taba irinsa a jihar ba tsawon shekaru 30 da kafuwarta.
Ya kara da cewa an samu gagarumin ci gaba a fannonin tsaro, gyaran ma’aikatan gwamnati, ilimi, lafiya da sauran bangarori, cewar rahoton Premium Times.

Source: Facebook
Ya ce:
“Ina godiya ga masu shirya wannan lacca da lambar yabo ta shekara-shekara. Wannan karramawa tana da matukar muhimmanci a gare ni, kuma za ta kara min kwarin gwiwar yin abubuwa fiye da haka domin al’ummata. Zamfara na kan hanyar ci gaba.”
Za a dauki sababbin malamai a Zamfara
An ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da cewa ta bude kofar ɗaukar malamai 3,050 domin cike giɓin malamai a makarantun gwamnati.
Kwamitin ɗaukar malaman ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da Babbar Sakatariyar Ma'aikatar Ilimi, Kimiyya da Fasaha ta jihar, Maryam Yahaya Shantali, ta sanya wa hannu.
A cewar kwamitin, manufar ɗaukar malaman ita ce ƙarfafa ilimin bai ɗaya ta hanyar tura ƙwararrun malamai zuwa makarantun da ke karkara da sauran wuraren da ake fama da ƙarancin malamai.
Asali: Legit.ng

