Sojoji Sun Shafe Mako Suna Ruwan Wuta kan 'Yan Ta'adda, an Kashe 69

Sojoji Sun Shafe Mako Suna Ruwan Wuta kan 'Yan Ta'adda, an Kashe 69

  • Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta kashe 'yan ta'adda 69 tare da ceto mutane 363 da aka yi garkuwa da su a ayyukan da ta gudanar cikin mako guda
  • Sojojin sun kuma kama mutane 49 da ake zargi da aikata laifi tare da tarwatsa matatun mai uku ba bisa ƙa'ida ba da kuma kwato lita 251,600 na ɗanyen mai da aka sace
  • Daraktan Yaɗa Labarai na DHQ, Manjo Janar Michael Onoja, ya ce soja ɗaya ya mutu yayin da wani ya jikkata a cikin ayyukan da aka gudanar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kashe 'yan ta'adda 69 tare da ceto mutane 363 da aka yi garkuwa da su a sassa daban-daban na ƙasar cikin mako guda.

Kara karanta wannan

"Mun bar ku da Allah': Mazauna Sokoto sun tura sako ga Gwamna kan rashin tsaro

Rundunar ta ce an samu nasarorin ne sakamakon hare-haren ƙasa, sama da ruwa da dakarun ke ci gaba da kai wa masu aikata laifi a sassa daban-daban na ƙasar.

Hafsun tsaro Najeriya a sojoji
Hafsun tsaro na kasa, CDS Oluyede yana magana da sojoji. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Twitter

Vanguard ta wallafa cewa daraktan Ayyukan Yaɗa Labaran Tsaro na DHQ, Manjo Janar Michael Onoja, ya bayyana hakan yayin da yake bayar da rahoton ayyukan sojojin, inda ya ce an kuma kama mutane 49 da ake zargi da aikata laifi.

An ceto mutane 31 daga daji

Onoja ya ce a ranar 31 ga Yuli, dakarun Operation Hadin Kai sun dakile yunƙurin wasu 'yan ta'adda na yin garkuwa da fararen hula a hanyar Buratai zuwa Kamuya da ke ƙaramar hukumar Biu ta jihar Borno.

Ya ce sojojin sun bi sawun maharan zuwa yankin Mangari-Dora, inda suka ceto mutane 31 da suka haɗa da maza 22, mata biyar da yara huɗu.

Sojojin sun kuma kwace motoci huɗu da babur ɗaya da ake zargin na 'yan ta'addan ne.

A wani samame da aka gudanar a kusa da gadar Amuda a ƙaramar hukumar Gwoza ta Borno, sojoji sun ceto mata biyu da yara biyu da aka tsare tun lokacin noma na shekarar 2023 a wani sansanin 'yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Dalilin Najeriya na bude ƙofar tuba ga 'yan bindiga a Najeriya

An kama wasu mutane a jihohi

Rundunar ta ce tsakanin ranar 2 zuwa 4 ga Agusta, wasu iyalan waɗanda ake zargin 'yan ta'adda ne sun mika wuya ga sojoji, yayin da aka kama wasu a ƙananan hukumomin Gwoza, Konduga da Bama na Borno.

Haka kuma, mutane 20 sun mika wuya ga dakarun a Kwuari da ke ƙaramar hukumar Konduga.

Dakarun sojojin Najeriya
Hafsun tsaro na yi wa sojoji bayani. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Twitter

A ranar 3 ga Agusta kuma, sojoji sun kama wasu mutane biyu da ake zargin masu samar da kayan abinci da sauran kayayyaki ga 'yan ta'adda ne a Monguno, inda aka kwato kayan abinci da tanade-tanade da ake zargin za a kai wa 'yan ta'adda a Kukawa.

Adadin 'yan ta'adda da dakarun Najeriya suka kashe sun kai 69 a rahoton da rundunar tsaro ta fitar a karshen makon nan a Abuja.

Gargadin Najeriya kan tsaron Saudi

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Najeriya ta yi Allah wadai da harin da mayakan Houthi na Yemen suka kai kan wuraren fararen hula a yankin Najran na Saudiyya.

Kara karanta wannan

Bayan wata 6 a hannun yan bindida, mutane 176 da aka sace a Kwara sun kubuta

Ma'aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta ce harin da ya jikkata fararen hula, ciki har da mata da yara, ta ce hakan take dokokin jinƙai na ƙasa da ƙasa ne.

Gwamnatin ta kuma bayyana damuwa kan ƙara tsanantar rikicin tsakanin Houthi da Saudiyya, inda ta yi kira ga dukkan ɓangarorin da su yi taka-tsantsan tare da mutunta dokokin ƙasa da ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng