Allah sarki: Yan gida daya su 2 sun rasu cikin sa’o’i 24 a jihar Borno (hotuna)

Allah sarki: Yan gida daya su 2 sun rasu cikin sa’o’i 24 a jihar Borno (hotuna)

Wani dan Najeriya mai suna Haruna Moda Maina Asaga ya nuna alhini akan mutuwar kannasa guda biyu. Mutumin ya yayi rashi na kaninsa da kuma kanwarsa, Usman da Asha Modu Mai a, a Maiduguri, jihar Borno.

An tattaro cewa kanin Haruna ya rasu a ranar Litinin, 23 ga watan Satumba, bayan fama da rashin lafiya sa’o’i 24 bayan yar’uwarsu Aisha ta rasu a ranar Lahadi, 22 ga watan Satumba.

Mutumin ya je shafinsa na Facebook domin sanar da wannan mummunan labara mai cike dab akin ciki. Ya yi alhinin rashin yan uwan nasa, inda ya bayyana yadda yake matukar kewansu.

Allah sarki: Yan gida daya su 2 sun rasu cikin sa’o’i 24 a jihar Borno (hotuna)
Allah sarki: Yan gida daya su 2 sun rasu cikin sa’o’i 24 a jihar Borno
Asali: Facebook

A rubutun da Haruna ya wallafa a shafin Facebook, ya nuna bakin ciki kan rashin kanwarsa, inda ya bayyana yadda suka shaku da kannen nasa.

Yace mutane da dama sun zata abokai ne shi da marigayiya kanwarsa, ba wai yan’uwan juna ba.

KU KARANTA KUMA: Kotun daukaka kara ta jingine hukunci akan karar da Dino Melaye ya shigar

Haruna ya kuma bayyana cewa ya rasa kannensa uku, Aisha, Zara, Ali da mahaifinsu shekara biyar da ya gabata. A washegarin ranar, Haruna yayi kira ga abokansa da suyi wa dan uwansa, Usman addu’a, wanda ke fama da rashin lafiya.

Yan sa'o'i bayan nan, sai Haruna ya bayyana cewa Usman ya rasu. Mutumin ya wallafa labari mai taba zuciya game da rasa ahli byar cikin shekara biyar, harda kannansa biyu da suka mutu cikin kwana biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel